Yadda wadanda aka yi garkuwa da su suka shafe kwanaki 53 sun cin ciyawa

Yadda wadanda aka yi garkuwa da su suka shafe kwanaki 53 sun cin ciyawa

  • Wasu da aka yi garkuwa da su a Zamfara sun ce sun rika cin ciyawa na tsawon kwana 53 don rashin abinci
  • Gwamnatin jihar Zamfara tabbatar da ceto kimanin mutane 185 daga hannun masu garkuwa da mutane
  • Daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ta bayyana cewa kimanin mutane 17 sun mutu saboda yunwa

Zamfara - Wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na jihar Zamfara sun koma cin ciyawa domin kada su mutu a yayin da wadanda suka sace su suka rasa abincin ba su.

Daya daga cikin wanda abin ya faru da su wacce ta ce sunanta Iklima Murtala, ta yi ikirarin cewa mutane 17 sun mutu saboda tsananin yunwa, ruwaiyar Daily Trust.

Yadda wadanda aka yi garkuwa da su suka shafe kwanaki 53 sun cin ciyawa
Taswirar Jihar Zamfara. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Gwamnati za ta cigaba da ragargazan 'yan bindigan

Kara karanta wannan

Bayan sa'o'i 4, layukan MTN sun dawo aiki, yan Najeriya sun yi korafi

Da ya ke karbar wadanda aka ceto a madadin gwamnati, sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Balarabe ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Gwamnati za ta cigaba da ragargazan 'yan bindigan har sai sun gaji sun ajiye makamai sun mika wuya."

Kwamishinan 'yan sanda a jihar ta Zamfara, Ayuba Elkana, ya ce saboda matsin lambar da rashin abinci, 'yan bindigan sun tsinci kansu a mawuyacin hali.

Ya ce:

"A halin yanzu suna matukar shan wahala kuma ba su iya aikata abubuwan da suka saba yi domin mun dakile su."

Da ya ke magana da Daily Trust, kakakin gwamnan jihar, Zailani Bappa, wanda ya tabbatar cewa an sako mutum 185 da aka yi garkuwa da su ya ce gwamnati na kulawa da magungunansu.

A cewarsa:

"Mutane 185 aka ceto. Abin farko da muke yi a Zamfara idan an ceto mutane shine kai su asibiti don duba lafiyarsu. Ana duba su don ganin ko sun kamu da cuta yayin tsare su. Wadanda ke da matsala gwamnati za ta biya kudin maganinsu har su warke kafin a sallame su.

Kara karanta wannan

Zamfara na fama da 'yan gudun hijira 700,000, gidaje 3,000 sun halaka, Matawalle

"A kan kuma basu abinci, tufafi da sauran kulawa yayin da suke hannun gwamnati. Bayan sun warke, a kan yi musu gwajin kwakwalwa da magani saboda halin da suka shiga hannun 'yan bindigan. Idan an musu magani sun warke sai a sada su da iyalansu su cigaba da rayuwa."

Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe mutum 19, ciki har da ƙananun yara, sun ƙone shaguna da gidaje

A wani rahoton, kun ji 'yan bindiga sun halaka mutane 19 ciki har da yara sannan sun kona gidaje da shagunan mazauna kauyen Kuryar Madaro da ke jihar Zamfara a daren Talata.

Premium times ta ruwaito yadda su ka kai farmakin washegarin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkana, ya kai wa ‘yan sandan musamman da suke aiki wuraren hanyar Shinkafi zuwa Kaura Namoda ziyara.

Kauyen Kuryar Madaro a karkashin karamar hukumar Kaura Namoda yake amma ya na da iyaka da Zurmi da Shinkafi, wurin da ta’addanci ya fi yawaita a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Hotunan wani gidan azabtarwa da aka gano, an ceto maza da yara 47 da aka ɗaure da mari

Asali: Legit.ng

Online view pixel