Bayan sa'o'i 4, layukan MTN sun dawo aiki, yan Najeriya sun yi korafi
- Mutane sun tabbatar da dawowar layukansu bayan awanni hudu sun kasa amfani da su
- Yayinda suka ce sun yi asarar kudade, wasu sun ce sun wahala matuka
- Wasu kuwa sun yi addu'an Allah ya takaita irin wannan fitina
Bayan sa'o'i hudu da daukewa layukan kamfanin MTN a fadin tarayya, Legit ta samu labari daga majiya mai tsoka kuma ta tabbatar da cewa an gyara kuma sun dawo aiki.
Yan Najeriya sun yi korafi kan yadda layukan wayoyinsu na MTN suka daina aiki da yammacin ranar Lahadi, 9 ga watan Oktoba, 2021.
Tun misalin karfe 3 na rana mutane suka fara fuskantar matsala wajen kira da hawa yanar gizo.
Wannan ya tada hankulan wasu da dama sakamakon toshe layukan sadarwan da ake yiwa kwanakin nan a jihohin Arewa.
Mutane da dama sun yi korafin cewa shin me ya sa kamfanin bai yiwa mutane bayani saboda su san abinda yake faruwa ba.
Ga jawabin mutanen Najeriya:
Abdulrauf Ahmad Musa yace:
Alhmdllh network yadawo a ko'ina
Dan Hassan Jikan Dudu yace:
In sun gama gyarawa subamu hakuri ta hanyar antayo mana data 500
Jaafar Muhammad Sani yace:
Abin da yaban haushi sai da zanyi transfer naga yaki yi duk wani enquiry yaki gashi Bani da kudi sannan ba ATM
Muhammad Auwal Usman Tal'udu yace:
Ashe haka mutanen zamfara sukeji chab to allah y bamu zaman lfy
Jamilu Gizzna yace;
Munsha wahala fa komai ya tsaya
Asali: Legit.ng