Kwana daya bayan jefa 'dansa kurkuku, Kotun ta sake watsawa AbdulRashid Maina kasa a ido

Kwana daya bayan jefa 'dansa kurkuku, Kotun ta sake watsawa AbdulRashid Maina kasa a ido

  • Kotun tarayya ta sake watsi da bukatar AbdulRasheed Maina
  • Wannan na zuwa ne kwana daya bayan jefa babban 'dansa gidan yari
  • Ana zargin AlbdulRasheed Maina da badakalar biliyoyin naira na yan fansho

Abuja - Alkalin babbar kotun tarayya dake Abuja ya yi watsi da bukatar tsohon shugaban kwamitin sauyin harkar fansho, AbdulRasheed Maina, na cigaba da kare kansa da hujjoji.

A ranar 6 ga Agusta, Maina ya shigar da bukata kotu cewa a sake dubawa hukuncin ranar 16 ga Yuli, 2021 a bashi daman cigaba da kare kansa.

Alkali Lauyan gwamnati, Farouk Abdullahi, ya ce sam ba zai yiwu ba, ya yi kira ga kotu tayi watsi da bukatar saboda hakan ya sabawa ka'idojin kotu, rahoton Independent.

A hukuncin da Alkali Abang ya yanke ranar Juma;a, yace:

Read also

2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya

"Bukatar da mai kare kansa ya shigar ba tada tsoka, saba ka'idojin kotu ne kuma na yi watsi da ita."
"Shari'ar ranar 16 ga Yuli inda mai kare kansa ya rufe kare kansa na nan kuma bai daukaka kara ba, saboda haka ba zai iya zuwa yanzu yace a sake budewa ba."
"An bashi daman daukaka kara amma bai yi ba. Su tuhumi kansu."

Kwana daya bayan jefa 'dansa kurkuku, Kotun ta sake watsawa AbdulRashid Maina kasa a ido
Kwana daya bayan jefa 'dansa kurkuku, Kotun ta sake watsawa AbdulRashid Maina kasa a ido
Source: UGC

An yankewa Faisal Maina hukuncin shekaru 14 a gidan kaso

Babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja ta yanke wa Faisal, dan gidan AbdulRasheed Maina, tsoohon shugaban hukumar fansho, hukuncin shekaru 14 a gidan gyara hali.

Alkali Okon Abang, wanda ya yanke hukuncin ya kama Faisal Maina da laifuka uku da hukumar EFCC ta zargesa da shi.

Read also

Femi Adesina: Ya dace a ce Sanata Abaribe ya na can ya na shakawata a gidan fursuna

Har yanzu ana cigaba da shari'ar mahaifin.

Manyan laifuka 3 da suka jawo aka daure Faisal Maina shekaru 14 a gidan yari

1. Halatta kudin Haram

A hujjojin da hukumar EFCC ta gabatar, an ce Faisal ya halatta kudin haram ta hanyar cin kudin da yasan haramtattu ne da mahaifinsa ya sace.

2. Hada kai wajen sace kudin al'umma

A bangare na biyu, an tuhumi Faisal da hada kai da mahaifinsa wajen kirkirar asusun banki na karya a bankin UBA domin karkatar da kudade, wanda hakan babban laifi ne a dokar kasa.

3. Tserewa doka yayin bincike

A sashe na uku kuwa, Faisal ya tsere zuwa kasar waje bayan ba da belinsa, wanda tuni ya daina halartar kotu don zaman shari'ar da ake gudanarwa.

Wadannan, da sauran wasu dalilai su suka jawo kotu ta garkame matashin tsawon shekaru 24 a gidan yari, amma zai kwashe shekaru 14 a ciki saboda wsau dalilai na doka, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel