Rashin Aikin Yi: Kana cikin waɗan da suka jawo Najeriya ta zama haka, Adesina ya maida ma Atiku Martani
- Mai baiwa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yaɗa labari, Mr. Femi Adesina ya maida kakkausan martani ga tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar.
- Adesina ya ce karfa ya manta ya buga nashi wasan na tsawon shekaru takwas a kasar nan kuma munga abinda ya yi
- Ya ce ba zai yuwu dan yanzun yana jam'iyyar hamayya ba ya koma ya wanke kansa yana yanke ma wasu hukunci.
Mr Femi Adesina, mai baiwa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, ya ce tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar na cikin waɗan da suka ɓata Najeriya.
A martani da ya maida masa kan magan-ganun da ya yi kwanan nan, Adesina ya ce "Atiku ba zai iya tsame hannunsa daga yadda Najeria ta zama ba."
KARANTA ANAN: Wa ya kamata yayi kayan daki? Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Atiku, wanda shine ɗan takarar shugaban kasa ƙarkashin jam'iyyar PDP a zaɓen 2019, ya ce a ƙarƙashin mulkin Buhari Najeriya ta kama hanyar lalacewa.
Yana mai cewa, Buhari bashi da ƙwarewar da zai mulki ƙasar, kuma dole ne 'yan Najeriya su taimaka ma gwamnatin don su tseratar da kansu.
Atiku ya kuma caccaki wasu kudirorin Buhari, yana mai cewa yawaitar marasa aikin yi a Najeriya ya wuce tunani, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Amma lokacin da yake maida masa martani a shirin gidan talabishin na 'Channels TV', Adesina yace:
"Idan zaka iya tunawa lokacin da ake shirye-shiryen zaɓen 2015, ya yin da APC ke tallata yan takarar ta, a lokacin a dadin da Buhari ya yi aiki dashi na mara sa aikin yi a ƙasar ya kai 30 miliyan, kuma mafiyawancin su matasa ne, ya kuma yi alƙawarin gwamnatinsa za ta yi wani abu akai."
"Wannan a wancan lokacin kenan 2014/2015. Kada kazama kamar kifin rijiya mana wanda ya fito yanzun. Dama can akwai rashin aiki a ƙasa."
Tsohon mataimakin Shugaban ƙasa ne shi na tsawon shekaru takwas, kuma yanzun yana ɓangaren hamayya, ba zamu ɗauki duk abinda ya faɗa gaskiya ne ba.
KARANTA ANAN: Ku cire mu a jerin masu son ballewa daga Najeriya, jihohin Kudu ga masu son kafa Biafra
Babban abin da zamu tambayeshi shine:
"Lokacin mulkinsu da shi da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, in suka kai Najeriya, kuma ina suka barta?" inji Adesina.
Adesina ya kara da cewa, naga wasu bidiyoyi a kafar sada zumunta shi da kansa yana cewa mutane sun amshi ayyukan tiriliyoyi a mulkinsu amma basu yi komai ba
"Tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar na cikin waɗanda suka gurɓata Najeriya," cewar Adesina.
Adesina ya kara da cewa, ba zai yuwu ya cire kansa ba, ya koma gefe yana yanke hukunci.
Ya yi nashi na tsawon shekaru takwas kuma sun bar mulki inda suka barshi "Ba zai yuwu ya koma gefe ya wanke kansa ba shi kaɗai."
A wani labarin kuma Okorocha ya sha mugun duka a hannun basarake a cikin jirgin sama
Basaraken ya daga sandarsa ne yayi kokarin rafka wa Rochas sakamakon wata jiƙaƙƙiya da suke da ita tun yana kan mulki
Kamar yadda ganau suka tabbatar, al'amarin ya faru ne a tashar jirgin saman Sam Mbakwe dake Owerri a ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng