Sheikh Gumi ga 'yan Arewa: Hanyoyin da za ku zauna lafiya da 'yan bindiga

Sheikh Gumi ga 'yan Arewa: Hanyoyin da za ku zauna lafiya da 'yan bindiga

  • Sheikh Gumi ya bayyana wasu hanyoyi da 'yan Arewa za su bi wajen tabbatar da zama lafiya da 'yan bindiga
  • Wannan na zuwa ne yayin da hare-haren 'yan bindiga ke kara kamari a yankunan Arewa maso yamma
  • Mutane da yawa na zargin malamin da zama mai magana da yawun 'yan bindiga da kuma tausaya musu

Kaduna - Babban malamin addinin Islama, Ahmad Gumi, ya shawarci mutanen yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da ta’addanci kan yadda za su zauna lafiya tare da ‘yan bindigar da ke mamaye dazuzzukan su.

Malam Gumi ya ce mutane za su iya habaka "alakar juna da 'yan bindiga ba tare da an cutar da su ba", PRNigeria ta ruwaito

Sheikh Gumi ga 'yan Arewa: Hanyoyin da za ku zauna lafiya da 'yan bindiga
Sheikh Gumi da tawagar 'yan bindiga | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

An nakalto malamin yana fadi yayin da yake gabatar da lacca a jami'ar ABU da ke Zariya a ranar Alhamis cewa:

Kara karanta wannan

An yi jana'izar mahaifin kakakin majalisar Zamfara da ya rasu a hannun 'yan bindiga

“Alakar da nake da ita da 'yan bindiga ta kasance mai sauki saboda ko yaushe ina ‘shiga wurinsu.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ku gana dasu a wurarensu ta kofa

Daya daga cikin shawarwarin Sheikh Gumi, ya ambaci cewa, ya kamata mutane su saki jiki suke zuwa wurin da 'yan bindiga suke, inji rahoton Premium Times.

Da yake amsa tambayoyin dalibai a wajen laccar, Gumi ya yi bayanin cewa:

“Ina shiga wurinsu ta kofa, ba taga ba. Idan kuka bi ta kofar, za ku shiga ku dawo lafiya,
"Idan mutane suka saurari 'yan bindiga, za su zama masu yin watsi da duk hanyoyin tashin hankali".

Wani dalibi ya tambayi dalilin da ya sa 'yan bindigan ba sa sace shi a lokacin da ya ziyarci maboyarsu da yawa.

Malam Gumi ya yi bayanin cewa:

“Lokacin da muka gana da su, ba ma magana, muna ba su makirufo don yin magana ko da na awa daya ne.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama mutumin da ke taimakawa masu garkuwa karɓar kuɗin fansa

“Lokacin da muka fara zuwa gare su, mun ga cewa suna rike da takardar bindigoginsu (makamai) a shirye don yin harbi. A lokacin da muka gama taronmu, za su ba da makamansu kuma muna daukar hotuna.
“Don haka wannan shine ikon hulda da dan adam wanda shine abin da muke karantawa anan a matsayin masana kimiyyar zamantakewa. Wannan ita ce hanya.”

Bi da su cikin mutuntawa

Malam Gumi, jami'in soji mai ritaya, ya ce ya sami damar samun kwarin gwiwar 'yan bindigar ne saboda yana:

"Daukar su a matsayin mutane kuma yana girmama su".
“Wannan shine girmamawa da nake ba su. Na ce ku zo, ku zo ku zauna tare da ni. Zo ku zauna. Ina so in ji daga gare ku. Da wannan girmamawa, za ku iya samun kan Bafulatani.
“Don haka kada ku yi mamaki, idan kuna kyautata masa, idan kuna shirye ku saurare shi, idan kuna kokarin fahimtar matsalar sa, idan kun sanya kafafun ku cikin takalmin sa, zai saurare ku, za ku iya zuwa daji ku dawo lafiya, in Allah ya so.”

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi

Mista Gumi ya ziyarci wasu 'yan ta'adda a maboyar dajin su kuma ya shawarci gwamnati da ta tattauna da su domin kawo karshen ta'addanci a yankin.

Shin Gumi mai tausayawa 'yan bindiga ne?

An zargi malamin da 'tausaya wa 'yan bindiga, wadanda ke gallazawa iyalai da al'ummomi da yawa ta hanyar munanan hare-harensu, garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kashe-kashen ba gaira ba dalili, amma ya musanta hakan.

Maimakon haka, ya ce damuwar sa ita ce kasarsa, jiharsa da bil'adama wanda ya sanya shi daukar shawarar tattaunawa ta lumana da 'yan bindigar.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da wasu shugabanni a arewacin kasar sun sha tattaunawa da 'yan bindiga a jihohinsu a baya amma matakin bai yi nasara ba wajen kawo karshen matsalar.

Yanzu gwamnan na Zamfara ya janye daga tattaunawar ya kuma amince da farmakin soji da ke gudana.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da takwaransa na jihar Neja, Abubakar Sani, a koda yaushe suna adawa da tattaunawa da 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

Kasurgumin shugaban 'yan bindiga ya tona asirin 'yan uwansa, ya nemi gafara

A wani labarin, Goma Samaila, shugaban gungun masu garkuwa da mutane a yankin Rigachukum ta jihar Kaduna, ya bayyana sunayen mambobin kungiyar sa, Daily Trust ta ruwaito.

Mutumin mai shekaru 47, wanda rahotanni ke cewa ya dade yana tafka ta'annuti, ya yi magana kan wasu ayyukansa da adadin kudin da ya karba a matsayin kudin fansa.

A wani faifan bidiyo, an ga Samaila yana rokon gafara yayin da daya daga cikin jami'an tsaron da ya kama shi ke tambayarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel