Kasurgumin shugaban 'yan bindiga ya tona asirin 'yan uwansa, ya nemi gafara
- Kasurgumin dan bindigan da aka kama ya fallasa sunayen wasu da yake aiki dasu a daji
- Ya kuma roki jama'a su yafe masa, inda ya ce shi dai ya rantse ba zai sake irin wannan aikin ba
- Ya kuma bayyana irin kudaden da ya karba na fansa daga wasu mutanen da ya yi garkuwa dasu
Kaduna - Goma Samaila, shugaban gungun masu garkuwa da mutane a yankin Rigachukum ta jihar Kaduna, ya bayyana sunayen mambobin kungiyar sa, Daily Trust ta ruwaito.
Mutumin mai shekaru 47, wanda rahotanni ke cewa ya dade yana tafka ta'annuti, ya yi magana kan wasu ayyukansa da adadin kudin da ya karba a matsayin kudin fansa.
A wani faifan bidiyo, an ga Samaila yana rokon gafara yayin da daya daga cikin jami'an tsaron da ya kama shi ke tambayarsa.
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ina rokon jinkai da gafara; Ba zan sake aikata irin wannan laifin ba."
Dangane da wasu ayyukan da ya yi, ya ce:
“Mutum na farko da muka yi garkuwa da shi shine Abdul; sun biya kudin fansa N200,000; akan Alhaji Umaru, mun karbi N500,000, Wani kuma Alhaji Birau; sun biya jimillar naira miliyan uku sannan dayan kuma shine Alhaji Ibrahim wanda ya biya N700,000. ”
Samaila ya kuma bayyana sunayen wasu daga cikin ‘yan kungiyar.
“A cikin Rigachikun, akwai Yusuf, Sale, Gomi, Nasiru, Tukur, Banki, Magaji.
“Sannan a yankin Kirama, akwai Musa, Kadi, Oria, Ibrahim, Bala, Rebo, Gaia, Malan, Osama, Babangida, Abubakar da Sule. Ba zan iya tuna sunan wanda ya bar mu ya koma wurin Babangida, Suleiman da Sule.”
Sojin Najeriya sun cafke kasurgumin shugaban 'yan bindiga mai suna Goma Sama'ila
Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasarar cafke shugaban ‘yan bindiga da barayin shanu, Alhaji Goma Sama’ila.
Legit.ng Hausa ta tattaro daga jaridar SaharaReporters cewa, an damke Samaila ne a jihar Kaduna da yammacin Juma’a 24 ga watan Satumba.
Rahotannin shaidun gani da ido sun nuna cewa Sama’ila ne ke da alhakin shirya satar shanu da dama a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.
An ce yana cikin wasu ayyunkan barna na garkuwa da mutane da dama a fadin jihohin.
Jihar Kaduna tana ci gaba da shan fama da barnar masu garkuwa da mutane, kisan gilla da satar shanu daga 'yan bindiga.
Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara
A wani labarin, alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.
Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.
Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.
Asali: Legit.ng