NSCDC ta kama mutumin da ke taimakawa masu garkuwa karɓar kuɗin fansa

NSCDC ta kama mutumin da ke taimakawa masu garkuwa karɓar kuɗin fansa

  • Jami'an NSCDC a jihar Enugu sun yi nasarar damke wani mutum da yake aiki tare da masu garkuwa da mutane
  • Mutumin ya ce masu garkuwan sukan saka kudi a asusunsa na banki, sannan ya cire kasonsa ya tura musu wani asusun daban
  • An kuma kama shi tare da bindigar kirar pistol ta gargajiya, wayoyin salula biyu da wani ganye da ake zargin wiwi ne

Enugu - Jami'an hukumar NSCDC a jihar Enugu sun kama wani mutum da ke aiki tare da masu garkuwa da mutane a Legas kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Danny Manuel, mai magana da yawun hukumar NSCDC a Enugu ya ce an kama mutumin dauke da katin ATM uku, wayoyin salula biyu, wani ganye da ake zargin wiwi ne da wani bindiga na gargajiya.

Kara karanta wannan

Fallasar handama: An matsa wa Buhari lamba kan ya bincike Bagudu, Obi da sauransu

NSCDC ta kama mutumin da ke taimaka wa masu garkuwa karɓar kuɗin fansa
Taswirar Jihar Enugu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Ya ce sunan wanda ake zargin Manuel Oguamanam da aka kama a WTC Estate a Enugu misalin karfe 2 na rana bayan dalibai da ke dawowa daga makaranta sun hange shi yana yi wa wasu fashi da bindigarsa pistol.

Manuel ya ce:

"Da ake masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa yana aiki tare da gungun masu garkuwa da mutane a Legas.
"Ya bayyana cewa masu garkuwar na saka kudi a asusunsa na banki, shi kuma zai ciro kudin, ya cire kasonsa sannan ya tura musu a wani asusun ajiyar.
"Ya kuma bayyana cewa wasu matasa sun masa fashi a unguwar hakan yasa ya tanadi bindiga domin idan ya gansu ya rama abin da suka masa.
"Ya ce daya daga cikin wayoyin nasa ne amma ya gaza yin bayanin yadda ya samo wayan android din ta biyu."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sallami ma'aikata 286 daga aiki

Rahoton na Daily Trust ya ce Manuel ya bawa mazauna Enugu tabbacin cewa NSCDC a shirye ta ke ta yi aiki da sauran hukumomin tsaro don basu kariya a jihar.

Hotunan Mutane 5 Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƙwararrun Mafarauta Suka Kama a Kogi

A wani labarin daban, kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi sun yi nasarar kama mutane biyar 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane, LIB ta ruwaito.

An kama mutane biyar din da ake zargi a safiyar ranar Talata a Atami, wani gari da ke wajen Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumban shekarar 2021.

King Habib, babban hadimi ga shugaban karamar hukumar Okehi a bangaren watsa labarai, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, yana mai cewa tawagar sun dade suna adabar mutane a titin Okene-Lokoja da Okene-Auchi a jihar Kogi State.

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: