Sokoto: Jerin sunayen mutum 19 da Yan bindiga suka aike wasikar neman kudin fansansu N20m
Sakamakon toshe layukan sadarwa a wasu jihohin Arewa maso yamma, yan bindiga sun kasa tuntubar iyalan wadanda suka sace ta waya, yanzu sun koma rubuta wasika.
Wannan sabon salo ya bayyana ne a jihar Sokoto inda yan bindiga suka aikawa Dagacin Burkusuuma a karamar hukumar Sabon Birni.
A cikin wasikar, yan bindigan sun bukaci Dagacin ya nemi kudi daga wajen iyalan wadanda suka sace da abokansu na arziki.
A wasikar dake dauke sunayen mutum 19, yan bindigan sun bukaci daya daga cikin wadanda suka sace ya bayyana halin da suka ciki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abinda wasikar ke kunshe da shi
A wasikar da Legit ta gani, an bayyana sunayen wadanda aka sace da kuma kudi N20m da ake bukatar kudin fansa.
Ga jerin sunayensu:
Maza
1. Yahaya
2. Bello Sani
3. Maharazu Mamman
4. Naziru Saidu
5. Lawali Nano
6. Abdullahi M Makau
7. Ashe Sani Mamman
8. Mustafa Abdullahi
9. Hussaini Ladan Samaila
Mata
1. Rashida Abdullahi
2. Rahila Abdullahi
3. Hana M isah
4. Hauwa
5. Maryam Sani
6. Hadiza Labaran
7. Jimma Maidabo Gatawa
Yara
1. Safiya A Sani
2. Aisha Labaran
Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Neja
Wani rahoton gidan talbijin na AIT ya kawo cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe sojoji biyu a wani hari da aka kai garin Kagara da fadar Sarkin, a jihar Neja.
Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a garin Minna, babbar birnin jihar, jim kadan bayan ya ziyarci sojoji goma sha biyu da suka jikkata wadanda ke karbar magani a asibitin Ibrahim Badamasi Babangida.
Gwamnan ya kuma ce wasu daga cikin sojojin da suka jikkata suna samun kulawar likitoci a wani asibiti da ke Kaduna, sashin Hausa na BBC ya kuma ruwaito.
Gwamnan a cikin wata sanarwa daga Babbar Sakatariyar Yada Labarai, Mary Berje, ya ce babu takamaiman adadin wadanda suka mutu.
Asali: Legit.ng