Yadda 'yan sandan Zamfara suka kama 'yan bindiga 69 da masu hada baki da su

Yadda 'yan sandan Zamfara suka kama 'yan bindiga 69 da masu hada baki da su

  • A ranar Lahadi, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana yadda ta kama ‘yan bindiga 21 a jihar
  • Har ila yau, ta kama masu taimaka mu su guda 69 sakamakon sintiri da binciken da su ka yi a watan Satumba
  • Jami’in hulda da jama’an rundunar, SP Muhammad Shehu ne bayyana hakan ga manema labarai a Gusau

Zamfara - A ranar Lahadi, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana yadda ta samu nasarar kama mutane 21 da ake zargin ‘yan bindiga ne da su ka addabi jihar tare da masu taimaka musu guda 69 duk a cikin watan Satumba.

SP Muhammed Shehu, jami’in hulda da jama’an hukumar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau, inda yake lissafo tarin nasarorin da jami’an tsaro su ka samu a jihar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka

Yadda 'yan sandan Zamfara suka kama 'yan bindiga 69 da masu hada baki da su
Yan sandan Nigeria. Hoto: Vanguard Ngr
Asali: Facebook

Shehu ya ce sun halaka manyan ‘yan bindiga 5

Kamar yadda ya bayyana, sun halaka shu’uman ‘yan bindiga 5 da jami’an tsaro su ka bayyana su na nema ido rufe.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, ya bayyana cewa:

“Tun bayan gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya samar da sababin dabarun kawo karshen rashin tsaro a jihar, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun cigaba da bin hanyoyin kawo karshen ‘yan bindiga da sauran miyagun mutane dake jihar.
“Sakamakon yadda jami’an tsaro su ka jajirce kuma su ka dage, an samu nasarori da dama don yanzu haka an halaka ‘yan bindiga sannan kuma hari, kashe-kashe da garkuwa da mutane duk sun rage a watan da ya gabata.

Kara karanta wannan

2023: Ai ba a yin dole a siyasa – Tsohon Gwamnan Arewa ya yi wa Gwamnonin Kudu raddi

“Hanyoyin da gwamnan ya samar sun dakatar da ‘yan bindiga daga samun abinci, man fetur, magunguna har da sauran ababen bukatun su.
“Yanzu haka an dakata daga biyan su kudaden fansa duk sakamakon tsaron da gwamnan ya sa a jihar, yanzu haka babu hanyar sadarwa tsakanin ‘yan bindiga da masu ba su bayanai na musamman.”

Yanzu haka an ceto wadanda ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su 200

Ya kara da bayyana yadda yanzu haka mutanen da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su suka zama ayyuka manya gare su don haka su ka dinga sakin su, bayan ‘yan sanda sun dage da neman su.

Kamar yadda Vanguard ta bayyana, tsaron da gwamnatin ta samar ya kara bunkasa tsaro a birane ta hanyar dakatar da ta’addanci irin garkuwa da mutane, fashi da makamai, kwacen motoci, balle gidaje da sauran su.

Shehu ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

“Ayyukan jami’an tsaro ya taimaka wurin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ga kauyaku da birane don yanzu haka ‘yan bindiga a firgice suke.
“Sakamakon ayyukan ‘yan sandan, yanzu haka an kama takadaren ‘yan bindiga 21 da su ka addabi jihar sannan an halaka 5 daga cikin su.”

Ya kara bayyana cewa:

“Yan sanda sun samu nasarar mayar da hare-hare 4 sakamakon haka ‘yan bindiga da dama su ka raunana. Sannan yanzu haka an kama masu kai mu su labarai, an yi bincike akan su kuma an yanke mu su hukunci.
“An samu nasarar ceto mutane 200 daga hannun masu garkuwa da mutane kuma tuni sun koma wurin ‘yan uwan su."

Hotunan Mutane 5 Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƙwararrun Mafarauta Suka Kama a Kogi

A wani labarin daban, kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi sun yi nasarar kama mutane biyar 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane, LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Matashi mai shekaru 21 ya jagoranci fashi a gidan maƙwabcinsa

An kama mutane biyar din da ake zargi a safiyar ranar Talata a Atami, wani gari da ke wajen Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumban shekarar 2021.

King Habib, babban hadimi ga shugaban karamar hukumar Okehi a bangaren watsa labarai, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, yana mai cewa tawagar sun dade suna adabar mutane a titin Okene-Lokoja da Okene-Auchi a jihar Kogi State.

Asali: Legit.ng

Online view pixel