Ganawar gwamnonin Arewa: Abubuwa 5 masu muhimmanci da suka cimma a taron

Ganawar gwamnonin Arewa: Abubuwa 5 masu muhimmanci da suka cimma a taron

A farkon makon nan ne gwamnonin Arewa suka zauna domin tattauna matsalolin yankin da kuma kokarin kawo ci gaba da kuma sauyi a bangarori daban-daban na kalubalen da yankin ke fuskanta.

A ranar Litinin, 27 ga watan Satumba, kungiyar gwamnonin Arewa ta yi taro a Kaduna don tattaunawa kan muhimman batutuwan da suka shafi yankin Arewa.

Bayan taron, shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya fitar da wata sanarwa mai kunshe da matsayar su.

Wannan rubutu na Legit.ng Hausa yana nuni ga manyan abubuwan da gwamnoni 19 daga yankin arewa suka cimma.

Ganawar gwamnonin Arewa: Abubuwa 5 masu muhimmanci da suka cimma a taron
Taron gwamnoni da sarakunan Arewa | Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

1. Shugabancin 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daya daga cikin manyan abubuwan da aka cimma a taron ya shafi zaben 2023 yayin da yankin kudancin ke fafutuka don samar da wanda zai maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Kungiyar ta lura cewa a baya wasu gwamnonin Arewa sun goyi bayan kudu don samar da shugaban Najeriya a 2023 don inganta hadin kai da zaman lafiya a kasar.

Sai dai, gwamnonin Arewa sun ce baki daya sun yi Allah wadai da kalaman da kungiyar gwamnonin kudu ta yi na cewa tilas mulkin kasar ya tafi kudu a 2023.

A cewarsu, kalaman na gwamnonin kudu ya sabawa kundin tsarin mulki.

2. Harajin Kan Kayayyaki (VAT)

Gwamnonin kudanci bayan wani taro na baya-bayan nan sun fitar da wata sanarwa da ta goyi bayan tara harajin VAT daga jihohi maimakon gwamnatin tarayya.

Wannan furucin nasu na zuwa ne a yayin da ake takaddama kan shari’a tsakanin jihar Ribas da hukumar tara kudaden shiga ta tarayya (FIRS) kan wanda ya kamata ya karbi harajin.

Sai dai, a cikin batutuwansu, gwamnonin na Arewa sun ce takwarorinsu na kudancin kasar suna rikita batun harajin sayarwa da na VAT.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Sun bayar da hujjar cewa idan kowace jiha ta kafa dokarta ta VAT, za a sami karbar harajin da yawa wanda zai haifar da hauhawar farashin kayayyaki da durkushewa a kasuwanci tsakanin jihohi.

Sai dai gwamnonin Arewa sun ce ba za su kara yin magana kan takaddamar haraji ba saboda har yanzu lamarin yana gaban kotu.

3. Tsaro a yankin arewa

Haka kuma gwamnonin Arewa sun tattauna kan yanayin tsaro a yankin. Sun lura cewa akwai bukatar ci gaba da aiki tare da hadin gwiwa tsakanin su da gwamnatin tarayya, sun kara da cewa an samu wasu nasarori a lamarin.

Sun kuma yaba da hare-haren da ake ci gaba da kaiwa kan 'yan ta'adda musamman a yankin tare da karfafawa sojoji da sauran hukumomin tsaron gwiwa da su ci gaba da gudanar da ayyukansu don ba da damar magance matsalolin tsaro a cikin kankanin lokaci.

Sun kuma bukaci sarakunan gargajiya a yankin da su bada tasu gudummawar wajen zakulo 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin PDP na shirin yin wani muhimmin taro kan karba-karba

4. Shan miyagun kwayoyi a Arewa

Gwamnonin arewa sun kuma lura da mummunan halin da ake ciki na yaduwar miyagun kwayoyi da shaye-shaye tsakanin matasa masu yawa a yankin.

Don haka, sun yi kira ga dukkan matakan gwamnatoci da al'ummomi da su tashi tsaye wajen kawo karshen wannan bala'i.

5. Kiwo a fili

A cikin abin da ake ganin martani ne kai tsaye ga zartar da dokar hana kiwo a fili daga gwamnonin kudanci, gwamnonin Arewa sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta daukar mataki kan Shirin Inganta Kiwon Dabbobi na Kasa.

A cewarsu, shirin zai zama mai ba da gudummawa wajen sauyi daga tsarin kiwo a fili kamar yadda ake yi a Arewa zuwa tsarin killacewa na zamani.

Majalisar dattawa ta nemi Buhari ya fitar da N300bn don gyaran tituna a Neja

A wani labarin, Majalisar dattijai a ranar Talata ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da Naira biliyan 300 a matsayin kudin taimakon gaggawa don gyara munanan hanyoyi a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Jagoran kungiyar yakin neman zaben Tinubu na kasa ya ajiye aiki

Wannan kuduri na babban zauren ya biyo bayan wani kudiri kan lalacewar hanyoyi a fadin jihar Neja da toshe hanyoyin ta hanyar nuna rashin amincewa da direbobin tirela da direbobin tanka suke yi a cikin kwanaki hudu da suka gabata.

Mataimakin Babban Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Sabi Abudullahi, mai wakiltar Neja ta Arewa ne ya kawo kudirin, in ji rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.