2023: Gwamnonin PDP na shirin yin wani muhimmin taro kan karba-karba

2023: Gwamnonin PDP na shirin yin wani muhimmin taro kan karba-karba

  • Gwamnonin PDP sun sanar da cewa kwamitin raba kujerar takara da Gwamna Ifeanyi Okowa ke jagoranta ta shirya wata ganawa gabanin babban taronsu na kasa
  • Rahotanni sun bayyana cewa, tuni aka aika da takardar sanarwar ganawar ga gwamnonin kafin babban taronsu
  • Rahoton ya ci gaba da nuna cewa membobin jam'iyyar sun rarrabu kan batun raba mukamin shugabancin jam'iyyar na kasa, yana mai cewa ana ci gaba da tattaunawa

FCT, Abuja- Gwamnonin Jam’iyyar PDP za su yi taro a ranar Laraba, 29 ga Satumba, a Abuja, don bayar da gudunmawa a shawarwarin da kwamitin karba-karba na Gwamna Ifeanyi Ugwanyi ya gabatar gabanin babban taron kasa na ranar 30 zuwa 31 ga Oktoba.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba, an aika da sanarwar ganawar ga dukkan gwamnonin da ake sa ran za su kasance a Abuja don muhimmin taron.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

2023: Gwamnonin PDP na shirin yin wani muhimmin taro kan rabon shugabanci
2023: Gwamnonin PDP na shirin yin wani muhimmin taro kan rabon shugabanci Hoto: PDP Governors in Action
Asali: Facebook

Jaridar a baya ta ruwaito cewa wata takarda da aka fallasa ta nuna cewa kwamitin karba-karban ya raba ofishin Shugaban jam’iyyar na kasa zuwa Kudu sannan ya mika ofishin sakataren jam’iyyar na kasa zuwa Arewa.

Wannan ya haifar da zanga–zanga daga membobin jam'iyyar na Kudu maso Gabas wadanda suka yi tsammanin za a karkatar da kujerar shugabancin jam’iyyar zuwa Arewa don ba Kudu damar samar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

Wani mamba a kwamitin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce:

“Har yanzu ana ci gaba da tattaunawa.
"Duk abin da muka amince da shi a karshe bayan tattaunawa da gwamnoninmu a ranar Laraba, za a gabatar da shi ga Kwamitin Aiki na Ƙasa wanda shi kuma zai kai shi ga Kwamitin Zartarwa don tabbatarwa."

Kara karanta wannan

Bikin 'yancin kai: FG ta tsaurara matakan tsaro, za ta rufe sakatariya a ranar Alhamis 30 ga wata

Hakanan, ana sa ran taron na gwamnonin PDP karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto zai tattauna batun kwamitin sulhu da Sanata David Mark ke jagoranta kan wasu batutuwan da suka shafi kalubalen shugabanci a jam'iyyar, Daily Trust ta ruwaito.

2023: Arewa za ta tashi da tikitin shugaban kasa a PDP, Yarbawa da Shugaban Jam'iyya

A gefe guda, mun ji a baya cewa yayin da ake shirin zaben sababbin shugabannin jam’iyyar PDP na kasa, ‘yan siyasar Kudu maso yamma suna neman kujerar shugaban jam’iyya.

Jaridar Daily Trust tace jam’iyyar PDP za ta tsaida wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023 ne daga jihohin yankin Arewacin Najeriya.

Haka zalika jam’iyyar adawar za ta fito da shugabanta na kasa daga cikin jihohin kudancin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng