Shugabancin 2023: Jagoran kungiyar yakin neman zaben Tinubu na kasa ya ajiye aiki
- Gwagwarmayar neman Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya shiga takarar shugaban kasa na 2023 yana kara karfi a yankin kudu maso yamma
- Da yawa daga cikin abokan tsohon gwamnan na Legas yanzu suna hada karfi da karfe don ganin ya zama shugaban kasa a 2023
- Daya daga cikin irin waɗannan mutane shine jagoran kungiyar Bola Ahmed Tinubu na ƙasa, Aliyu Lawal Saulawa, wanda kwanan nan ya yi murabus don bai wa shugaban APC na ƙasa goyan baya
Abuja - Domin mayar da hankali kan Kungiyar Tallafa wa Tinubu (TSG), Aliyu Lawal Saulawa, mai kula da kungiyar Bola Ahmed Tinubu (BAT) na kasa, ya sauka daga mukaminsa.
Saulawa, wanda ya bayyana haka a Abuja a ranar Litinin, 27 ga Satumba, ya bayyana cewa ya yi murabus daga ofishin ne domin ya hada kai da TSG da kuma tabbatar da shugabancin Tinubu 2023 ya zama gaskiya, jaridar Leadership ta ruwaito.
Tsohon shugaban na BAT ya lura cewa wadanda ke goyon bayan jagoran jam'iyyar APC na kasa mutane ne masu son ci gaba da hadin kan Najeriya da ci gabanta.
Ya ce zabubbukan da suka gabata sun bayyana yadda mutane daga kudu maso yamma suka mika wuya ga Tinubu don haka, lokaci yayi da zai samu goyon bayan da ake bukata gabanin zaben shugaban kasa mai zuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Saulawa ya ce:
“Duk kun san cewa a Najeriya muna cikin tsarin Arewa maso Kudu da Kudu maso Arewa. Don haka abin da muke gani daga zabubbukan da suka gabata shine mika kai ga mutanen kudu maso yamma musamman karkashin ikon Bola Ahmed Tinubu.
“Don haka wadannan su ne mutanen da ke son kiyaye hadin kai da ci gaban ‘yan Najeriya ga matasanmu masu tasowa. Don haka ba mu da wani zabi face mu zagaye Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa."
Shugabancin 2023: Yakasai ya lissafa 'yan siyasa 3 na kudu da ka iya nasara a matsayin dan takarar APC
A wani labarin, Salihu Tanko Yakasai, tsohon hadimin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) yana yankin kudu maso yamma, ba a kudu maso gabas ba.
Tsohon hadimin gwamnan ya yi ikirarin cewa shiyyar kudu maso gabas ba ta da lambar siyasa da kuma dan takarar da ke da karfi don jan kuri'u a fadin kasar a zabe mai zuwa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Yakasai ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, lokacin da ya bayyana a matsayin bako a gidan talabijin na Arise.
Asali: Legit.ng