Mai dakin Basarake ta kai karar shi wajen ‘Yan Sanda, tace Sarki ya damfare ta N150m

Mai dakin Basarake ta kai karar shi wajen ‘Yan Sanda, tace Sarki ya damfare ta N150m

  • Mai dakin Mai martaba Sarkin Orile-Kemta, Adetokunbo Tejuoso, tana karar shi
  • Halima Oniru tace Mai gidan na ta ya karbi wasu kudi kimanin N150m hannunta
  • Oba Ade Tejuoso ya karyata Gimbiyar, yace kudin da ya karba ba su kai haka ba

Ogun - Halima Oniru, mai dakin Mai martaba Sarkin kasar Orile-Kemta, a garin Odeda, jihar Ogun, tana karar mai gidanta, Sarki Oba Adetokunbo Tejuoso.

Daily Trust tace Halima Oniru tana zargin Mai martaba Oba Adetokunbo Tejuoso da laifin karbar wasu kudi daga hannunta, ta hanyar yin yaudara da karya.

Wannan mata ta rubuta takarda zuwa ga shugaban ‘yan sanda na kasa, ta hannun lauyanta, J. S Agada.

Lauyan ya shaida wa IGP cewa Mai martaban ya nemi kudi da sunan za ayi kasuwanci ta karkashin wani kamfaninta, Haleems Integrated Services Ltd.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Oba Tejuoso: An je gaban IGP

Halima Oniru ta kuma sanar da jami’an tsaro cewa Oba Tejuoso ya karbi aron Naira miliyan 150 a hannunta, yana yi mata karyar yana neman sarauta a jihar Ogun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adetokunbo Tejuoso
Sarkin Orile-Kemta, Adetokunbo Tejuoso Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

A karshe Oniru ta auri Tejuoso

Oniru take cewa Basaraken ya taba nuna mata wasu takardun cinikin bogi domin ya damfare ta.

“Haka ya yi tayi mani karyar kasuwanci iri-iri, ya rika neman kudi a hannuna, har abin ya kai miliyoyi.”
“A karshe dai muka tare a matsayin mata da miji. A lokacin da muke zaman aure ne sai na fahimci asalin halinsa na damfara da aikin yaudarar mutane.”
“A dalilin haka, sai na tunkare shi, sai ya fara yi mani duka, yana barazanar zai kashe ni. A karshe ya kore ni daga gidan, ba tare da na dauki kaya na ba.”

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Jaridar tace Mai martaba Oba Tejuoso ya musanya zargin, yace karya matar tayi masa, yace sam kudin da Oniru take bin shi bashi ba su kai Naira miliyan 150 ba.

Jirgi ya kashe masu su a Borno

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka ji cewa ana zaune kalau, jirgin yakin Sojoji ya hallaka Bayin Allah akalla 20 a wani kauye da ke kusa da tafkin Chadi a Borno.

Tsaustsayi ya rutsa da wadannan mutane da suka shiga Kwatar Daban Masara domin su kama kifi.

Source: Legit

Online view pixel