Jirgin Sojoji ya sake yin tuntube, ya buda wa mutane 20 wuta suna kama kifi a Borno

Jirgin Sojoji ya sake yin tuntube, ya buda wa mutane 20 wuta suna kama kifi a Borno

  • Ana zargin jirgin sojoji ya kashe masunta a kauyen Kwatar Daban Masara
  • Tun safiyar ranar Lahadi abin ya faru, amma sai yanzu ne ake jin labarin
  • Jirgin yakin Najeriya ya kashe mutane yayin da yake neman ‘yan ta’adda

Borno - Akalla masunta 20 aka kashe da tsautsayi a wani hari da rundunar sojojin Najeriya suka yi kokarin kai wa ‘yan ta’adda a wani kauyen jihar Borno.

Jami’an sojojin Najeriya sun shaida wa AFP cewa jirgin yakin sojojin sama ya yi luguden wuta a kauyen Kwatar Daban Masara a tafkin Chadi a kan iyaka.

Wannan kauye da ya hada Najeriya da kasashen Nijar, Chadi da Kamaru ya yi kaurin suna wajen ba ‘yan ta’addan Islamic State West Africa Province, mafaka.

Jaridar Daily Trust tace an yi kuskure wajen hallaka ‘yan ta’addan ISWAP a Kwatar Daban Masara, aka kashe wasu mutane kimanin 20 da ke kama kifi.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Rahoton yace ba da dade wa ba ne sojojin ‘yan ta’addan suka janye hanin da suka yi na kama kifi, suka kyale mazauna yankin suyi su domin su samu na abinci.

Jirgin Sojoji
Jirgin yakin NAF Hoto: www.aa.com.tr
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda abin ya faru

Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa duk wanda ya je su a wannan wuri, ya kai kan shi ga halaka domin ‘yan ta’adda ke zama a kauyen.

A cewar wannan mutumi, babu yadda za ayi sojojin da ke jiragen sama su iya banbamce ‘yan ta’adda da sauran mutanen gari da suka zo wurin domin su.

“Bayanan da muke samu shi ne adadin wadanda aka hallaka sun haura mutane 20.”

Wani wanda yake sana’ar kama kifi a Kwatar Daban Masara, ya sanar da AFP cewa da kimanin karfe 6:00 na safe aka kai harin da ya kashe mutane kimanin 20.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Hakan na zuwa ne kusan makonni biyu bayan wani jirgin sojojin sama ya hallaka mutane a Yobe. Rashin kyawun layin waya ya sa ba a samu labarin da wuri ba.

Kisan gillan Jos

Idan kuna biye da mu, kuna da labari cewa a watan Agusta ne wasu Miyagu suka tare hanyar Jos, suka hallaka mutane rututu yayin da suke shirin koma wa Ondo.

An fara shari’a da mutanen da suka kashe wadannan Bayin Allah da suka je addu’a a Bauchi

Asali: Legit.ng

Online view pixel