'Yan Bindiga Sun Kutsa Wata Unguwa a Abuja, Sun Sace 'Ya'yan Ma'aikacin FG Biyu Da wasu Mutane 3

'Yan Bindiga Sun Kutsa Wata Unguwa a Abuja, Sun Sace 'Ya'yan Ma'aikacin FG Biyu Da wasu Mutane 3

  • Wasu bata gari da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari Unguwar Chukuku da ke Abuja
  • Mutanen dauke da bindigu sun kutsa gidan wani ma'aikacin hukumar gwamnatin tarayya sun sace yaransa biyu
  • Har wa yau, sun kuma shiga wani gidan inda suka sace ma'aikaciyar jinya a asibiti da wasu mutanen biyu

FCT, Abuja - Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun kai hari unguwar Chukuku da ke karamar hukumar Kuje na babban birnin tarayya Abuja daga daren ranar Lahadi zuwa asubahin Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa maharan sun sace mutane biyar, cikin mazauna unguwar da suka kutsa domin kai hari.

'Yan Bindiga Sun Kutsa Wata Unguwa a Abuja, Sun Sace 'Ya'yan Ma'aikacin FG Biyu Da wasu Mutane 3
Birnin Tarayyar Nigeria, Abuja. Hoto: Daily Trust
Source: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai farmaki coci, sun sheke mai bauta

Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun rika barin wuta a yayin da suke kutsawa cikin unguwar domin su firgita mutane.

Wani mazaunin wanda ya nemi a boye sunansa ya ce 'yan bindigan sun tafi gidan wani ma'aikaci a hukumar gwamnatin tarayya suka sace yaransa biyu, Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna unguwar sun kuma ce 'yan bindigan sun tafi wasu gidajen inda suka sace wata ma'aikaciyar jinya da wasu mutane biyu.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine ta ce bata da masaniya kan afkuwar lamarin.

Akwai Yiwuwar Malamin Addinin Musulunci Sheikh Gumi Ɗan Leƙen Asirin Ƴan Bindiga Ne, In Ji OPC

A wani labarin daban, kungiyar Yarabawa ta Oodua Peoples Congress, OPC, reshen jihar Oyo karkashin jagorancin Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa, Gani Adams ta ce ziyarar da Gumi ya kai ta bazata jihar Oyo cin fuska ne ga Yarbawa baki daya.

Read also

Mutane da dama sun hallaka yayin da miyagun yan Bindiga suka farmaki barikin Sojoji a Sokoto

A yayin zantawarsa da manema labarai a karshen mako, Rotimi Olumo, jagorar OPC a jihar Oyo ya ce Gumi yana wuce gona da iri kuma ya gargade shi ya kiyayi yankun Kudu maso Yamma na kasar Yarbawa, SaharaReporters ta ruwaito.

A cewar Olumo, ziyarar Gumi babban barazana ce ta tsaro ga dukkan yankin Yarbawa domi ba su ga amfanin hakan ba sai dai cin fuska da kokarin wofintar da mutanen kudu maso yamma.

Source: Legit

Online view pixel