Akwai Yiwuwar Malamin Addinin Musulunci Sheikh Gumi Ɗan Leƙen Asirin Ƴan Bindiga Ne, In Ji OPC

Akwai Yiwuwar Malamin Addinin Musulunci Sheikh Gumi Ɗan Leƙen Asirin Ƴan Bindiga Ne, In Ji OPC

  • Kungiyar Yarbawa ta OPC reshen jihar Oyo ta gargadi Sheikh Gumi ya kiyayyi yankin kudu maso yamma
  • Kungiyar ta nuna rashin jin dadinta kan ziyarar da ya kai yankin tana mai cewa akwai yiwuwar leken asiri ya tafi yi wa yan bindiga
  • Rotimi Olumo, shugaban OPC na jihar Oyo ya jinjinawa jagoran kungiyar na kasa Gani Adams bisa jagoranci na gari

Oyo - Kungiyar Yarabawa ta Oodua Peoples Congress, OPC, reshen jihar Oyo karkashin jagorancin Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa, Gani Adams ta ce ziyarar da Gumi ya kai ta bazata jihar Oyo cin fuska ne ga Yarbawa baki daya.

A yayin zantawarsa da manema labarai a karshen mako, Rotimi Olumo, jagorar OPC a jihar Oyo ya ce Gumi yana wuce gona da iri kuma ya gargade shi ya kiyayi yankun Kudu maso Yamma na kasar Yarbawa, SaharaReporters ta ruwaito.

Read also

Shugabancin 2023: Yakasai ya lissafa 'yan siyasa 3 na kudu da ka iya nasara a matsayin dan takarar APC

Akwai Yiwuwar Malamin Addinin Musulunci Sheikh Gumi Ɗan Leƙen Asirin Ƴan Bindiga Ne, In Ji OPC
Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Gumi. Hoto: SaharaReporters
Source: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Olumo, ziyarar Gumi babban barazana ce ta tsaro ga dukkan yankin Yarbawa domi ba su ga amfanin hakan ba sai dai cin fuska da kokarin wofintar da mutanen kudu maso yamma.

Ya ce sukar da Gumi da tawagarsa ke yi wa Igoho alama ce da ke nuna sun zo wurin ne domin tsokar fada da cin fuskar Yarbawa a kasarsu, wadda OPC ba za ta amince da hakan ba.

A yi taka-tsantsan da Gumi, ta yi wa dan leken asirin 'yan bindiga ne, OPC

Ya yi kira da mutanen yankin kudu maso yamma su cigaba da sa ido domin Gumi ba abin yarda bane.

OPC ta ce ziyarar ne Gumi zuwa yankin kudu lamari ne mai alamar tambaya, domin ana zargin ya zo ne a matsayin dan leken asiri na 'yan bindiga kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Read also

Yunwa ta fara fatattakar 'yan bindiga daga jihar Katsina, inji gwamna Masari

Olumo ya ce shugabannnin OPC na jihar Oyo sun gamsu da jagorancin Iba Gani Adams kan yadda ya ke gudanar da ofishin Aare Onakakanfo na kasar Yoruba da batun tsaro baki daya.

Ya kuma yaba wa gwamnonin yankin kudu maso yamma bisa kokarinsu na ganin an samu zaman lafiya a yankin, yana mai cewa mutanen yankin a shirye suke su bada hadin kai da jami'an tsaro don kiyayye rayuka da dukiyoyin al'umma.

Tsoho mai shekaru 84 da ya bar gida tsawon shekaru 47 ya dawo, ya nuna ɓacin ransa don matansa 2 sun sake aure

A wani labarin daban, wani tsoho mai shekaru 84, Peter Oyuk ya sha mamakin yadda matan sa 2 suka sake aure bayan ya yi tafiya tsawon shekaru 47.

Kamar yadda LIB ta ruwaito daga The Standard, mutumin ya bar kauyen Makale dake Malava bangaren Kakamega a shekarar 1974 lokacin yana da shekaru 37.

Read also

El-Rufai: Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan

Ya sanar da iyalan sa cewa ya tafi neman arziki don tallafa wa matan sa 2 da yaran sa 5 duk da dai bai sanar da su lokacin da zai dawo ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel