Hasashe: Garabasa 4 da Shehu Sani kan iya samu ta dalilin komawa PDP
Watanni bayan ficewa daga jam'iyyar PRP, Sanata Shehu Sani a yanzu shine sabon mamba na babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP.
Daily Trust ta tabbatar da ficewar Sani daga hannun hadiminsa na kusa, Malam Suleiman Ahmed a makon jiya.
Ahmed ya ce mai gidan nasa ya sauya sheka ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, lokacin da yake ganawa da wasu jiga-jigan PDP a Kaduna.
Shin me Sanata Sani zai samu da shiga jam'iyyar adawa ta PDP?
A shekarar 2015, an zabi sanata Shehu Sani don wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki. Ya kasance mai sukar lamirin da kalubalantar lamurra da dama.
2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu
Tsakanin 2015 da 2019, Sanata Sani ya yi fice a tsakanin takwarorinsa, wajen tsayawa a kan ra'ayoyinsa. Lokacin da lamari ya bukata, bai jin kunyar sukar jam’iyyarsa (APC).
Baya ga muhimman kudurori da da ya ba da gudunmawa, daya daga cikin abubuwan da suka fi jan hankalin Sanata Sani a Majalisar Dattawa shi ne yadda ya bayyana cewa shi da abokan aikin sa na karbar Naira miliyan 13.5 a kowane wata.
Sanatan a baya ya fito fili ya bayyana cewa akwai karancin lissafi game da yadda ake kashe kudade a kasar.
A wani yunkuri nasa, ya yi kira da a rage kudaden da ake biyan 'yan majalisar dattawan, yana mai cewa sune babban dalilin da yasa mutane suka zabi shiga siyasa kan kowane irin bangare na sana'a.
Ya shaida wa BBC cewa:
"Na yanke shawarar bude batun ne. Batu ne na dabi'a.
"Majalisar kasa tana daya daga cikin bangarorin gwamnati marasa gaskiya. Ya ja hankalina kuma na yanke shawarar fasa kwai sannan na bude sirrin majalisar ta kasa don jama'a su sani."
Duk da cewa Sanata Sani ya so ci gaba da hidima a majalisa, rikicin da ya barke tsakaninsa da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jawo masa rasa tikitin takarar sanata na jam'iyyar APC.
Ya zabi komawa wata karamar jam’iyya mai suna PRP, inda ya tsaya takara amma ya sha kaye a jam’iyyar.
Tun lokacin da ya sha kaye a shekarar 2019, tasirin siyasar Sani ya ragu sosai, inda ya zama "mai suka a kafafen sada zumunta".
A wani lokaci, Gwamna El-Rufai har ya taba zolayarsa, inda ya ce tsohon sanatan ya zama mai rubutun ra'ayi a yanar gizo.
Yanzu dai ya sauya sheka zuwa PDP, kuma akwai wasu abubuwa da hakan zai iya haifar masa.
Kara habakar siyasarsa da tasirinsa
PDP ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya kuma ita ce kadai jam'iyya a halin yanzu da za ta iya dakushe tasirin APC.
Da shiga PDP, Sanata Sani ya dawowa daga sukar gwamnati a kafafen sada zumunta zuwa tasirantuwar suka a siyasa mai tushe kuma da alama ya zama daya daga cikin manyan jagororin jam'iyyar a jihar Kaduna.
Yiwuwar samun tikitin Sanata a PDP
Kafin shekarar 2023, idan Sanata Sani yana da sha’awar komawa majalisar dattijai, yana da mafi kyawun damar samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyar adawa ta PDP.
Idan aka yi la’akari da wa’adinsa da ya gabata a Majalisar Dokoki, Shehu Sani da aka haifa a Kaduna zai taka muhimmiyar rawa idan ya koma Majalisar Dattawa.
Akwai manufofi da dama na gwamnati da ya soka da shawarwarin da ya bayar tun shekarar 2019. Komawa Majalisar Dattawa zai ba shi damar neman hanyoyin doka don aiwatar da sauye-sauye.
Yiwuwar samun tikitin gwamna a PDP
Maimakon komawa Majalisar Dattawa, Sanata Sani zai iya canza ra'ayi ya zuwa zabin tasayawa a matsayin dan kasa na daya a jihar Kaduna.
A shekarar 2023, abokin danbarwar siyasar Sani, Gwamna El-Rufai, ba zai yi takarar gwamna ba domin da ya gama wa'adi na biyu da kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.
Don haka, Shehu Sani na da damar iya tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa na 2023.
Nadin minista
Idan ya gaza samun kujerun siyasa da aka lissafa a sama, ana iya nada Sanata Sani minista muddin PDP ta kawar da APC mai mulki daga karaga a zaben 2023 mai zuwa.
Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40
A wani labarin, akalla jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar Enugu 41 aka kora daga jam’iyyar mai mulki a ranar Lahadi, 12 ga watan Satumba, sakamakon zargin karya tsarin dokar cikin gida.
A jawabinsa ranar Lahadi ga manema labarai kan matakin hukunta mambobin, shugaban kwamitin riko na APC a jihar, Ben Nwoye, ya ce mutanen da abin ya shafa sun shigar da kara a kan jam'iyyar ba tare da fara bin hanyoyin magance rikici ba a cikin gida ba.
Leadership ta rahoto cewa mambobin sun shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Abuja suna neman a cire Nwoye daga mukaminsa.
Sai dai shugaban ya bayyana cewa wadanda aka kora daga aikinsu ya sabawa sashi na 21 (D), sashe na V na kundin tsarin mulkin APC, in ji Vanguard.
Asali: Legit.ng