Hafsat Ganduje: Hotunan matar Ganduje ta koma Kano bayan EFCC ta bada belinta

Hafsat Ganduje: Hotunan matar Ganduje ta koma Kano bayan EFCC ta bada belinta

  • Hukumar yaki da rashawa na EFCC ta bada belin Hafsat Ganduje, matar gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje
  • Abdulazeez Ganduje, dan Hafsat na fari ne ya yi korafi game da mahaifiyarsa a wurin hukumar EFCC
  • Abdulazeez ya yi ikirarin cewa mahaifiyarsa ta karbe makuden miliyoyi daga wani mai gini da ke son sayan fili a Kano amma ta sayarwa wani daban filayen

Kano - An saki Hafsat Ganduje, matar gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje kan beli bayan hukumar yaki da rashawa da yi wa arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta kama ta.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa an kama Hafsat Ganduje ne a yammacin ranar Litinin aka kuma tsare ta na tsawon awanni a hedkwatar hukumar EFCC da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano

Hafsat Ganduje: Hotunan matar Ganduje da aka saki kan beli daga ofishin EFCC
Hafsat Ganduje yayin da ta dawo Kano daga ofishin EFCC. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hafsat Ganduje: Hotunan matar Ganduje da aka saki kan beli daga ofishin EFCC
Hafsat Ganduje yayin da ta dawo Kano daga ofishin EFCC a Abuja. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Ba a tabbatar ko a ofishin na EFCC ta kwana ba ko kuma ta sake komawa ne a safiyar ranar Talata, amma majiyoyi masu nagarta sun tabbatar cewa an ganta a ofishin EFCC a ranar Litinin da yamma da safiyar Talata.

Majiyoyi sun shaidawa Daily Nigerian cewa an bada belin ta a safiyar ranar Talata bayan ta cika ka'idojin belin da EFCC ta saka.

Hafsat Ganduje: Hotunan matar Ganduje da aka saki kan beli daga ofishin EFCC
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayin da ya dawo Kano tare da matarsa Hafsat Ganduje daga Abuja. Hoto: Daily Nigerian. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Jim kadan bayan bada belin, Hafsat Ganduje tare da mijinta gwamnan Kano da wasu iyalanta sun koma Kano a jirgin alfarma.

Dan Hafsat Ganduje na fari, Abdulazeez ne ya yi karar ta zuwa ofishin EFCC yana ikirarin cewa ta ta yi damfara a batun siyan fili da ya kai mata.

Dan nata ya yi korafin cewa wani mai gini ya bukaci ya taimaka masa ya siya wasu filaye a Kano inda ya bada daruruwan dalolin Amurka da kuma a kalla Naira Miliyan 35 a matsayin 'kudin taimaka masa samun filin'.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

Wani majiya da ke da masaniya kan lamarin ya ce:

"Amma bayan watanni uku, (mai ginin) ya gano cewa an sayar wa wani filayen da ya ke son siya don haka ya nemi a mayar masa da kudinsa."

Da Ɗumi-Ɗumi: EFCC Ta Kama Matar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje

Tunda farko, kun ji cewa hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama, Haftsat Ganduje, matar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan zargin rashaswa da rikicin fili da dan ta ya yi karar ta, Premium Times ta ruwaito.

An kama ta ne makonni bayan ta ki amsa gayyatar da hukumar ta EFCC ta yi mata.

Tunda farko dai EFCC ta gayyaci matar Gandujen zuwa hedkwatar ta a ranar 13 ga watan Satumba kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel