Hotunan jarumar Kannywood, Rahama Sadau, yayin da daliban Najeriya a Indiya suka karramata
- Jarumar Kannywood, Rahma Sadau ta gana da daliban Najeriya da suke karatu a Jami’ar Integral da ke kasar Indiya
- Hakazalika, jarumar ta yi godiya ga ma’aikatan jami’ar da sauran daliban makarantar bisa karamci da suka nuna mata
- A yayin taron an kuma karramata da lambar yabo wanda ta nuna matukar jin dadi a kan haka
Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Rahma Sadau ta gana da daliban Najeriya da suke karatu a Jami’ar Integral da ke kasar Indiya.
Rahama ce ta bayyana hakan a shafinta na Instagram inda ta nuna farin cikinta a kan wannan gayyata da ta samu daga daliban kasarta tare da gode ma ma’aikatan jami’ar.
Ta wallafa a shafin nata:
“Ina matukar farin ciki da alfaharin samun gayyata daga daliban Najeriya da ke karatu a Jami’ar Integral ta kasar Indiya. Na kasa boye farin cikina da wannan girmama da karamci.
"Ga ma’aikatan Jami’ar Integral University @integral_university__ liyafarku ta kasance mai daɗi abun soyuwa da godiya. Kuma ga ɗaliban wannan jami’a mai daraja masu ƙwazo waɗanda suka shirya wannan taro don girmama zuwana, kun sami matsayi na musamman a cikin zuciyata. Ina Godiya ga lambobin yabo da komai ...Soyayya da yawa ❤️"
Rahma Sadau ta saki hotuna tare da Vidyut Jammwal, da alamun zata fito sabon Fim din Indiya
A baya mun kawo cewa, shahrarriyar yar wasar kwaikwayon Hausa watau Kannywood, Rahama Sadau, ta saki sabbin hotunanta tare da shahrarren dan wasan Indiya watau Bollywood, Vidyut Jammwal.
Sadau wacce ta saki hotunan a shafinta na Instagram da yammacin Juma'a ta nuna cewa tana kasar Indiya yanzu haka.
Jarumi Vidyut Jammwal ne babban dan wasa a shirin Khuda Haafiz dake gudana.
Tsarin rayuwarta ba ta Musulunci bace da arewa, Matashi ya soki magoya bayan Sadau
A wani labarin kuma, wani dan Najeriya mai suna Abubakar Suleiman Idris, yace magoya bayan jarumar fina-finai, Rahama Sadaua, makiya Musulunci ne da yankin arewacin kasar nan.
Idris ya sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 18 ga watan Afirilu bayan wani George Onmonya Daniel ya jinjinawa jarumar a kan rabon kayan abinci da tayi ga mabukata.
Kamar yadda Abubakar yace, George da sauran magoya bayan jarumar a kan abinda ta raba duk makiya Musulunci ne da arewa saboda yanayin tsarin rayuwarta babu Musulunci a ciki balle kuma yankin arewa.
Asali: Legit.ng