Rahma Sadau ta saki hotuna tare da Vidyut Jammwal, da alamun zata fito sabon Fim din Indiya

Rahma Sadau ta saki hotuna tare da Vidyut Jammwal, da alamun zata fito sabon Fim din Indiya

  • Da yammacin juma'a, Rahama Sadau ta bayyana cikin hotuna tare da yan wasan Indiya
  • Hotunan sun nuna alamun cewa tana wajen daukar Fim ne
  • Rahama tana tare da wani shahrarren dan wasan Bollywood, Vidyut Jammwal

Shahrarriyar yar wasar kwaikwayon Hausa watau Kannywood, Rahama Sadau, ta saki sabbin hotunanta tare da shahrarren dan wasan Indiya watau Bollywood, Vidyut Jammwal.

Sadau wacce ta saki hotunan a shafinta na Instagram da yammacin Juma'a ta nuna cewa tana lasar Indiya yanzu haka.

Jarumi Vidyut Jammwal ne babban dan wasa a shirin Khuda Haafiz dake gudana.

Rahama Sadau tace:

": “Hello Bollywood . . . "
"Muna nan tare da Vidyut Jammwal “We Out Here with Vidyut Jammwal Vidyut Jamwalions’ #KhudaHafeezChapter2 #Day31"

Kalli hotunan: Shafa dama don ganin jerin hotunan

Ban yi imani da bayyana soyayya a fili ba, na fi son ta sirri, in ji Rahama Sadau

A baya, Rahama Sadau ta ce ba ta yi imani da bayyana soyayya da babbar murya ba kamar yadda ta fi so ta sanya rayuwar soyayyar ta zama sirri, Daily Trust ta ruwaito.

Ta bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ta yada a shafinta na Twitter, @Rahma_sadau ranar Juma'a.

“To dai, na fi son kiyaye shi shirri. Abu daya ne duniya ta san ku hakanan wani abu ne daban na "shi" (shi kadai) ya san kuma ya riski gaskiyar ki," kamar yadda ta wallafa.

Sadau, wacce ta yi suna a karshen shekarar 2013 bayan ta shiga masana’antar finafinai ta Kannywood tare da fim dinta na farko 'Gani ga Wane'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel