Dandalin Kannywood: Abun da ya hana ni sake yin aure - Jaruma Samira Ahmad
Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood mai suna Samira Ahmad ta fito ta bayyana babban dalilin da ya sa har yanzu ba ta sake yin aure ba.
Mun samu dai cewa jarumar da ke zaman tsohuwar matar shahararren mawakin nan kuma mashiryin fina-finai watau T. Y Shaba ta bayyana cewa yanzu haka miji nagari ne take ta nema domin ta sake yin aure.
KU KARANTA: Fim ya fi karatun jami'a wahala - Hauwa Yusuf
Legit.ng dai ta samu cewa jarumar a baya sun yi aure da jarumin fim din inda kuma har Allah ya albarkace su da samun diya mace a tsakanin su kafin zaman na su ya zo karshe.
'Yan fim dai da dama na shan suka wajen jama'a musamman ma akan maganar aure inda ake alakanta su da cewa ba su son zaman aure ko kadan, zargin da su kuma jaruman sukan karyata a ko da yaushe.
A wani labarin kuma, su ma fitattun fuskokin nan na wasan kwaikwayon Dadin Kowa da ake haskawa a tashar tauraron dan adam ta Arewa 24 kuma daya daga cikin 'yan biyun masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood watau Gimbiya da kuma Sa'adatu sun bayyana cewa suna addu'ar Allah ya kawo masu mijin aure suma.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng