Tsarin rayuwarta ba ta Musulunci bace da arewa, Matashi ya soki magoya bayan Sadau

Tsarin rayuwarta ba ta Musulunci bace da arewa, Matashi ya soki magoya bayan Sadau

- Wani matashi mai suna Abubakar Suleiman Idris yace babu Musulunci ko kishin arewa a tsarin rayuwar Rahama Sadau

- Matashin yayi wannan wallafar ne bayan wani George ya yabawa jarumar akan yadda ta raba tallafin kayan abinci ga mabukata

- Matashi Abubakar yace George ya yabeta ne saboda tsabar kiyayyar arewa da Musulunci wanda jarumar ke yi

Wani dan Najeriya mai suna Abubakar Suleiman Idris, yace magoya bayan jarumar fina-finai, Rahama Sadaua, makiya Musulunci ne da yankin arewacin kasar nan.

Idris ya sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 18 ga watan Afirilu bayan wani George Onmonya Daniel ya jinjinawa jarumar a kan rabon kayan abinci da tayi ga mabukata.

Kamar yadda Abubakar yace, George da sauran magoya bayan jarumar a kan abinda ta raba duk makiya Musulunci ne da arewa saboda yanayin tsarin rayuwarta babu Musulunci a ciki balle kuma yankin arewa.

"George, mun san zaka nuna goyon baya ko kuma ka rubuta labarai masu dadi a kanta saboda yanayin tsarin rayuwarta ba irin na arewa bane ko Musulunci. Kai baka kaunar arewa balle Musulunci," yace.

KU KARANTA: Ana sauran sa'o'i 2 daurin aure, mota ta bige ango, ya sheka lahira a Nasarawa

Tsarin rayuwarta ba ta Musulunci bace da arewa, Matashi ya soki masu goyon bayan Sadau
Tsarin rayuwarta ba ta Musulunci bace da arewa, Matashi ya soki masu goyon bayan Sadau. Hoto daga @Rahma_sadau
Asali: Twitter

KU KARANTA: A wurin liyafa, ango ya zabgawa amarya mugun mari, 'yan biki sun sha mamaki

A yayin da Onmonya ya tambaya matashin akan abinda yake nufi da tsarin rayuwar jarumar, sai yace yana nufin yadda take saka kaya.

"Yanayin saka kayanta na daya daga ciki kuma yadda take mu'amala shima haka. Kuma saboda 'yan arewa na kokawa da hakan ne yasa kake so kuma kake cigaba da nuna mata goyon baya saboda tsanar arewa," yace.

Sai dai Onmonya da wasu daga cikin magoya bayan jarumar sun caccaki matashin.

Wani Ibrahim Bature daga jihar Kano, ya zargi matashi Abubakar da munafinci tare da runtse ido idan ya ga 'ya'yan masu hannu da shuni ko manyan 'yan siyasa sun fito sanye da tufafi masu nuna tsiraici.

A wani labari na daban, masarautar Kano ta musanta siyar da filayen Gandun Sarki wadanda yasa hukumar yaki da rashawa ta jihar kano take tuhumar Sarki Aminu Bayero da shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar yaki da rashawan tana bincikar masarautar akan zargin siyar da filaye har kadada 22 dake Gandun Sarki a Dorayi Karama ta karamar hukumae Gwale dake jihar Kano tare da waskar da kudin zuwa aljihunsu.

Takardun karar da wani wanda ya siya filin, Alhaji Yusuf Aliyu ya shigar, ta bukaci kotun da ta dakatar da shugaban hukumar daga hana su aikin ginin da suka fara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel