Gwamnatin Buhari ta ce bata gama da Igboho ba, akwai sabbin tuhume-tuhume a kansa

Gwamnatin Buhari ta ce bata gama da Igboho ba, akwai sabbin tuhume-tuhume a kansa

  • Gwamnatin Najeriya ta ce akwai tuhume-tuhume da yawa da za ta iya shigarwa kan Sunday Igboho
  • Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar, SAN ne ya bayyana haka
  • Ya bayyana irin abubuwan da gwamnati za ta iya sake shigarwa kotu don tuhumar Sunday Igboho

Biyo bayan da wata kotu a jihar Oyo ta umarci a bai wa Sunday Adeyemo (Igboho) Naira biliyan 20, gwamnatin tarayya ta yi nuni da yiwuwar daukaka kara kan hukuncin.

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya Abubakar Malami, ya shaida wa manema cewa gwamnati na da damar daukaka kara kan hukunci ko kuma ta shigar da sabon tuhuma kan dan awaren Yarba Sunday Igboho, rahoton Premium Times.

Ya bayyana haka ne a yau Alhamis, 23 ga watan Satumba, 2021.

Malami ya yi bayanin cewa a cikin yanayin yin biyayya ga umarnin doka akwai wasu hakkoki da bukatun da ke hannun gwamnati, Punch ta kara da cewa.

Kara karanta wannan

Gwmnatin Buhari ta shirya kwato £200m da aka sace aka boye a Amurka

FG na iya gabatar da sabbin tuhume tuhume a kan Sunday Igboho - Malami
Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa | Hoto: saharareporters.com
Asali: Facebook

Malamai wanda kuma shine ministan sharia na Najeriya ya bayyana sabbin tuhume-tuhume da za a iya shigarwa inda yake cewa:

"Ciki har da hakkokin roko a kan hukunci, hade da hakkin shigar da kara don kebe hukuncin da aka dauka da oda.
"Kuma hakika, hade da yiwuwar cika wani sabon tuhuma idan da gaske ne ikon kotun da ake zargin ya bayar da wannan hukunci wani batu ne.
"Don haka, muna yin abin da ya dace ta fuskar duba doka kamar yadda ta wanzu sannan kuma muna aiki cikin yanayin doka don tabbatar da cewa an yi adalci kan abubuwan da a ke rikici tsakaninsu a bangarori."

FG ta ki halartar kotu don sauraran karar da Nnamdi Kanu ya shigar a kanta

A wani labarin, Babbar kotun jihar Abia a ranar Talata ta dage sauraron karar da ta shafi jagoran IPOB da aka tsare, Nnamdi Kanu zuwa 7 ga Oktoba, 2021, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yunwa ta fara fatattakar 'yan bindiga daga jihar Katsina, inji gwamna Masari

Alkalin kotun, Jastis KCJ Okereke, ya dauki wannan mataki ne yayin da fg da wasu mutane biyar da ake kara a shari’ar suka gagara gabatar da bayanansu kan karar da Kanu ya shigar gaban kotun, inda yake kalubalantar take hakkin sa da Gwamnatin Najeriya ta yi.

A cikin karar mai lamba HIH/FR14/2021, wadanda ake kara sun hada da Gwamnatin Tarayyar Najeriya (1), Babban Lauyan Tarayya (2), Babban Hafsan Sojoji (3), Sufeto Janar na 'Yan sanda (5), ​​Darakta Janar , Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (7) da wasu manya uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel