FG ta ki halartar kotu don sauraran karar da Nnamdi Kanu ya shigar a kanta

FG ta ki halartar kotu don sauraran karar da Nnamdi Kanu ya shigar a kanta

  • Wata kotu a jihar Abia ta zauna zaman karar da Kanu ya shigar kan gwamnatin Buhari
  • Kanu ya shigar da karar ne inda ya bayyana cewa, an zalunce shi da aka dawo dashi Najeriya
  • Ya nemi kotu ta bi kadunsa kan take hakkinsa da aka yi a matsayinsa na dan adam dan Najeriya

Abia - Babbar kotun jihar Abia a ranar Talata ta dage sauraron karar da ta shafi jagoran IPOB da aka tsare, Nnamdi Kanu zuwa 7 ga Oktoba, 2021, Punch ta ruwaito.

Alkalin kotun, Jastis KCJ Okereke, ya dauki wannan mataki ne yayin da fg da wasu mutane biyar da ake kara a shari’ar suka gagara gabatar da bayanansu kan karar da Kanu ya shigar gaban kotun, inda yake kalubalantar take hakkin sa da Gwamnatin Najeriya ta yi.

Kara karanta wannan

APC za ta wargaje idan aka fito da ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa inji Okorocha

A cikin karar mai lamba HIH/FR14/2021, wadanda ake kara sun hada da Gwamnatin Tarayyar Najeriya (1), Babban Lauyan Tarayya (2), Babban Hafsan Sojoji (3), Sufeto Janar na 'Yan sanda (5), ​​Darakta Janar , Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (7) da wasu manya uku.

Da Duminsa: FG ta ki halartar kotun don sauraran karar da Nnamdi Kanu ya shigar a kanta
Nnamdi Kanu shugaban IPOB | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

A baya Kanu ya shigar da kara ta hannun lauyan Aloy Ejimakor a makon jiya tare da neman a bashi N5bn a matsayin diyyar take hakkin sa da gwamnatin ta yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Karar ta ambaci kokarin barazana da rayuwar Kanu a jihar Abia tun a shekarar 2017, wanda shi ne dalilin da yasa ya tsallaka kasar. Daga karshe gwamnatin Najeriya ta kwamuso shi a kasar waje.

Ya roki kotun da ta bayyana cewa kamun sa, azabtar da shi da tsare shi sun sabawa tsarin mulki.

Ya kuma roki kotu da ta bayyana cewa kamo shi daga Kenya zuwa Najeriya, da kuma harin da sojoji suka kai masa a Abia a 2017, ya saba ka'ida ne kuma take hakki ne.

Kara karanta wannan

Shekaru 39 da bada kwangila, ba a soma aikin samar da lantarki a tashar Mambila ba

A zaman na yau, ya bayyana cewa daga cikin mutane takwas da ake kara, biyu ne kawai - DSS a Abuja da Umuahia - suka kawo martaninsu kan karar su ma din ba a kan lokaci ba.

Ba a samu bayanin komai daga sauran mutane shida da ake kara ba, wadanda suka hada da FG, AGF da Sojojin Najeriya.

Daga nan sai alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Oktoba domin bawa sauran wadanda ake kara damar gabatar da bayanan su.

Da yake yanke hukuncinsa na dage shari’ar, alkalin ya lura cewa Kanu zai sami wasu sassaucin hukunci a kan duk wanda ya ki amsa karar a kan lokaci.

Nnamdi Kanu ya maka kasar Kenya a kotu bisa laifin mika shi ga Najeriya

Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu, ya maka Kenya a kotu saboda mika shi ga gwamnatin Najeriya, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu karbuwa a jam'iyyun siyasa 17 na kudanci

Dan uwansa, Kingsley Kanunta ne ya shigar da kara a madadinsa, kamar yadda takardun kotu suka nuna.

A cikin korafin da gungun lauyoyin Luchiri suka gabatar, Kanu ya bayar da hujjar cewa kamun da aka yi masa a Kenya da kuma mika shi ga Najeriya a watan Yuni ya sabawa tsarin mulki.

Wadanda aka bayyana sunayensu a matsayin wadanda ake kara sune CS na cikin gida na Kenya, Daraktan Shige da Fice, Daraktan Binciken Laifuka, filin jirgin saman kasa da kasa na OCPD Jomo Kenyatta da Babban Lauyan Kasar ta Kenya.

Yan kudu: Son kai ne Buhari ya yi sansanin sojin ruwa a Kano bai yi a Bayelsa ba

A wani labarin, Dattijo kuma babban jigon kabilar Ijaw, Cif Edwin Clark, ya caccaki Babban Hafsan Sojojin Ruwa (CNS), Admiral Awwal Zubairu, kan shirin rundunar sojin ruwan Najeriya na kafa sansanin sojan ruwa a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Hasashe: Garabasa 4 da Shehu Sani kan iya samu ta dalilin komawa PDP

A wata budaddiyar wasika da ya aike ga CNS a ranar Litinin, 20 ga Satumba, Clark ya yi tir da amincewa da kafa sansanin sojojin ruwa a Kano, yana mai cewa matakin yana daya daga cikin ayyukan son kai da gwamnatin Buhari ke jagoranta.

Wani yanki daga cikin wasikar da jaridar The Punch ta wallafa ya ce:

"Cewa ana gina sabon sansanin sojan ruwa a tsakiyar sahel wanda duk duniya ta sani a halin yanzu na fuskantar barazanar hamada da ke yaduwa cikin sauri kuma ba tare da wani la'akari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel