Yunwa ta fara fatattakar 'yan bindiga daga jihar Katsina, inji gwamna Masari

Yunwa ta fara fatattakar 'yan bindiga daga jihar Katsina, inji gwamna Masari

  • Gwamnan jihar Katsina ya yi gargadin cewa, yunwa ta addabi 'yan bindiga don haka a kula
  • A cewarsa, 'yan bindiga za su fara shiga gonakan mutane suna girbe shukan da manoma suka yi
  • Ya bayyana haka ne a jiya Talata yayin wani taro da aka yi a jihar kan batutuwa da suka shafi tsaro

Katsina - Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya yi gargadin a kula game da komawar 'yan bindigan da yunwa ta fatattaka, zuwa garuruwa da yankuna don satar kayayyakin gona kafin lokacin girbi, Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamnan ya yi gargadin ne a ranar Talata 21 ga watan Satumba, a Katsina, a wani taron shawari da ya yi da Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Mohammed kan yanayin tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun hallaka kasurguman yan bindiga 5, tare da mabiyansu 23 a Zamfara

Taron ya samu halartar Shugabannin hukumomin tsaro na jihar, sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da na addini, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.

Yunwa ta fara fatattakar 'yan bindiga daga jihar Katsina, inji gwamna Masari
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar Masari:

"Saboda yunwa, 'yan bindiga suna tafiya zuwa al'ummomin da ke kusa da yankin dajin da suke ciki. Sun san cewa lokacin girbi na gabatowa kuma shirin su shine girbe amfanin gona da sace kayan abinci da manoma suka shuka."

Matakan gwamnati na aiki wajen fatattakar 'yan bindiga

A baya cikin rahoton TheCable, 'yan bindiga sun koma tambayar kayayyakin abinci a madadin kudin fansa sakamakon matsin lamba da suka samu daga jami'an tsaro a jihohi.

Gwamnan ya ce an fatattaki 'yan ta'adda a cikin jiharsa sakamakon matakan da aka sanya, gami da dakatar da hanyoyin sadarwa na wayar salula da hana sayar da albarkatun mai a gidajen mai da yawa.

Kara karanta wannan

Masari: Muna cin nasara kan 'yan bindiga, sojoji na gasa musu aya a hannu

Ya umarci shuwagabannin tsaro, da su farka daga bacci tare da addabar masu laifi, hadi da jaddada matsayinsa na cewa ba zai tattauna da 'yan bindiga ba.

Gwamna Masari ya bayyana cewa jihohin da aka fi fama da hare-haren 'yan bindiga sun yanke shawarar daukar mafarauta da 'yan banga 3,000 wadanda 'yan sanda za su horar da su don kare mazauna garuruwa.

Ya ce Katsina za ta dauki mafarauta 500 da ‘yan banga - 250 kowanne daga Katsina da masarautar Daura don kare al’ummomi daga hare-haren 'yan bindiga.

Ya kuma yi bayanin cewa mafarautan da ’yan bangan za su kasance cikin mazauna dindindin don kare mutane da dukiyoyinsu.

Musamman, ya ce, bayan kokarin sojoji, mafarauta da 'yan banga za su ci gaba da kare al'ummomin, tare da yaba hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da aka tura jihar wadanda, yace sun taimaka wa nasarorin da aka samu a kan 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garkuwa da wasu a Sokoto

Mai martaba sarkin Katsina, Kabir Usman, ya yabawa gwamnan kan sabbin dabaru na dakile rashin tsaro a jihar.

Basaraken, wanda ya ce yana adawa da tattaunawa da 'yan bindiga, ya yi kira ga ministan da ya ci gaba da samar da ingantaccen bayani kan yaki da rashin tsaro a kasar.

Sarkin, wanda ya ki amincewa da tattaunawa da 'yan bindiga, tare da biyan kudin fansa, ya yi kira ga jami'an tsaro da su kara kaimi wajen yaki da masu laifi.

'Yan bindiga sun tare motar 'yan sanda sun kashe jami'ai, sun bakawa motarsu wuta

A wani labarin, akalla ‘yan sanda uku aka kashe a garin Onitsha, jihar Anambra sakamakon harin 'yan bindiga.

Lamarin ya faru ne a hanyar Ukaegbu/Ezeiweka a Onitsha a safiyar Lahadi 19 ga watan Satumba, 2021.

An kuma kona wata motar sintiri kurmus ta jami'an da suka mutu. Wakilin Daily trust ya tattaro cewa wasu ‘yan sanda biyu sun jikkata a harin.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume: Kisar Kiyashin Da Sojoji Ke Yi Wa 'Yan Bindiga Ya Yi Dai-Dai

Asali: Legit.ng

Online view pixel