Kotu ta daure dan hadimin gwamna Tambuwal shekaru 4 a magarkama bisa laifin yada bidiyon batsa

Kotu ta daure dan hadimin gwamna Tambuwal shekaru 4 a magarkama bisa laifin yada bidiyon batsa

  • Alkalin kotun Majistare na jihar Sakkwato, Shu’aibu Ahmad, ya yankewa wasu samari uku hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari
  • An yankewa matasan masu suna Aminu Hayatu Tafida, Umar Abubakar da Mas’ud Abubakar Gidado hukuncin ne saboda yada bidiyon tsiraicin wata budurwa
  • Aminu ɗa ne ga mai ba gwamna Aminu Waziri Tambuwal shawara ta musamman kan saka hannun jari, Hayatu Tafida

Sakkwato - Babbar Kotun Majistare ta Sakkwato ta yanke wa wasu matasa uku, Aminu Hayatu Tafida, Umar Abubakar da Mas’ud Abubakar Gidado hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari saboda yada bidiyon tsiraicin wata mai shirin zama amarya.

Aminu ɗa ne ga mai ba gwamna Aminu Waziri Tambuwal shawara ta musamman kan saka hannun jari, Hayatu Tafida.

Kara karanta wannan

Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai

Kotu ta daure dan hadimin gwamna Tambuwal shekaru 4 a magarkama bisa laifin yada bidiyon batsa
Kotu ta daure dan hadimin gwamna Tambuwal shekaru 4 a magarkama bisa laifin yada bidiyon batsa Hoto: Thisday
Asali: UGC

An same su da laifuffuka da suka hada da taɓarɓarewa, aikata ba daidai ba, siyarwa da buga littafin batsa da watsa bidiyon tsiraici na daƙiƙa 18, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A cikin hukuncin da ya yanke, Alkalin kotun Majistare Shu’aibu Ahmad, ya lura cewa wannan ne karo na farko da wadanda ake kara suka aikata laifi wanda a yanzu sun fahimci illar abin da suka aikata.

An ba su zabin biyan tarar N400,000.

Ahmad ya ce:

"Na yi la'akari da roƙon kowanne mai ba da shawara da kuma buƙatar kiyaye al'umma daga irin wannan aikin.
“A kan abin da bai dace ba da kuma rashin mutunci, kowanne daga cikin wadanda ake tuhuma zai biya tarar N200,000 idan aka saba za su shafe shekaru biyu a gidan yari. A kan sayar da littafin batsa, kowannensu zai biya tarar N50,000 ko ɗaurin shekaru biyu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnati ta datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 na jihar Sokoto

"A kan hada kai wajen aikata laifi, kowannen su zai biya tarar N50,000 idan aka saba zai kasance daurin watanni shida."

Sai dai, ya umarci kowanne daga cikin wadanda ake kara da su biya N100,000 ga mai kara a matsayin diyya.

"Da fatan cewa, wannan hukunci zai zama izina ga wasu.”

Rahoton ya kuma kawo cewa mai shari'an ya ce lauyan wadanda ake kara na da damar daukaka kara kan hukunci idan ba su gamsu ba.

Da take jawabi jim kadan bayan yanke hukuncin, mahaifiyar wanda abin ya rutsa da ita, Hajiya Safiya Umar, ta bayyana gamsuwa da hukuncin, inda ta ce "bangaren shari'a ya tabbatar da cewa shine gatan talakawa."

An yi rikodin bidiyon da ake zargi ya shafi 'yar shekaru 16 a cikin shekarar 2017.

Alkali ya sabunta laifukan da ake zargin dan hadimin Tambuwal da wasu mutum 2

A baya mun ji cewa wata kotun majistare da ke zama a Sokoto ta kama wasu matasa da laifin yada bidiyon tsiraicin wata yarinya a kafafen sada zumuntar zamani.

Kara karanta wannan

An yi ram da wasu ma'aikatan asibiti a Gombe da laifin sace gidan sauron talakawa

Wadanda ake zargin sune wani Aminu Tafida, da mai ada shawara na musamman ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Umar Abubakar da Mas'ud Gidado.

Amma kuma wanda ake zargi na hudu mai suna Aliyu Shehu kangiwa an wanke shi saboda bashi da wata alaka da wannan laifin, Daily Trust ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel