An yi ram da wasu ma'aikatan asibiti a Gombe da laifin sace gidan sauron talakawa

An yi ram da wasu ma'aikatan asibiti a Gombe da laifin sace gidan sauron talakawa

  • An kama wasu ma'aikatan asibiti da suka karkatar da gidajen sauro a wasu yankunan jihar Gombe
  • An kamasu yayin da suke kokarin sayar da gidajen sauron a wata kasuwa a cikin jihar ta Gombe
  • Kwamishinan lafiya na jihar Gombe ya gargadi ma'aikata kiwon lafiya da su sani gidajen sauron na talakawa ne

Gombe - Ma’aikata bakwai na Ma’aikatan Kiwon Lafiya na Kananan Hukumomin Kwami da Billiri a Jihar Gombe a halin yanzu suna hannun ‘yan sanda saboda karkatar da 5,450 gidajen sauro masu magani (ITNs) da ake rabawa kyauta a al'ummomin su.

Gwamnatin jihar, tare da tallafi daga Asusun Duniya, Catholic Relief Serive da Shirin kawar da zazzabin cizon sauro sune masu tallafawa wajen rarraba gidajen sauron kyauta, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya a jihar Gombe, Dr Habu Dahiru, ya fadawa wani taron manema labarai a Gombe ranar Asabar cewa an cafke wadanda ake zargin ne a ranar 10 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Barin wuta ta sama: Gwamnan Yobe ya umurci asibitocin gwamnati da su kula da wadanda suka jikkata

An yi ram da wasu ma'aikatan asibiti a Gombe da laifin sace gidan sauron talakawa
Taswirar jihar Gombe | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Dahiru ya ce ITNs din ana raba su ne don rage zafin zazzabin cizon sauro a cikin jihar, musamman tsakanin bangarorin da suka fi rauni - mata da yara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya koka da cewa an karkatar da gidajen sauron "ba tare da nuna kishin kasa ba da kuma aikata laifuka don kawai son kai".

Ya ce:

“Kamun wadanda ake zargi ya yiwu ne ta hanyar ma’aikatan da aka dorawa alhakin kula da yadda ake gudanar da aikin don tabbatar da cewa gidajen sauron ba su shiga hannun da ba daidai ba.
“Wani dan leken asiri ya gano cewa an daura gidajen sauron a cikin babbar mota a cikin daga cikin kasuwannin Gombe da nufin karkatar da su.
“Bayan an samu labari, an sanar da 'yan sanda nan da nan kuma aka kama motar da ke dauke da gidajen sauron.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da 'yan bindiga sun mamaye murabba'in mita 1,129 na gandun dajin Najeriya

"An kama 'yan kasuwar da za su yi jigilar gidan sauron an kuma gano sauran wadanda suke hada baki."

Adadin da aka kwato

Neptune Prime ta ruwaito cewa, Dahiru ya ce an kwato daurin gidan sauro 100 daga Kwami yayin da aka kwato dauri tara daga Billiri, ya kara da cewa za a raba gidan sauron ga mutanen da suka dace a cikin kananan hukumomin biyu.

Kwamishinan ya yi gargadi game da sayar da gidajen sauron, yana mai jaddada cewa:

“Wadannan gidajen sauron na talakawa ne kuma dole ne a kai musu kyauta. Babu wanda zai biya kudi.''

Dahiru ya nuna jin dadinsa kan kokarin da 'yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya, mambobin hukumar tsaro ta NSCDC da sauran jama'ar da suka yi kokari wajen kama bata-garin.

Sarki a Arewacin Najeriya ya ce mata su karbi mulki a hannun Buhari a 2023 kawai

A wani labarin, Mai martaba Sarkin Keffi, Alhaji Shehu Yamusa III, ya yi kira ga matan Najeriya da su nuna sha’awarsu ta shugabancin kasa domin su gaji shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a shekarar 2023, yana mai cewa hakan ba zai gagara ba.

Kara karanta wannan

Hukuncin da Ya Dace Yan Najeriya Su Ɗauka Kan Shugabannin da Suka Gaza Cika Alƙawari, Tsohon Ministan Sadarwa

A cewarsa, ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da kabila ko alakar siyasa ba, dole ne su raba tunanin al’adu da siyasa don samar da mafi kyawun shugabanci a kasar, Punch ta ruwaito.

Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Jami'ar Jihar Nasarawa, ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis 16 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel