Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnati ta datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 na jihar Sokoto

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnati ta datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 na jihar Sokoto

  • Gwamnatin Sokoto ta sanar da katse hanyoyin sadarwa a ƙananan hukumomi 14 cikin 23 dake jihar
  • Gwamnan jihar, Aminu Tambuwal, shine ya sanar da haka ranar Litinin, yace gwamnatinsa ta samu sahalewar Pantami
  • Gwamnan yace miyagun yan bindiga da suka tsero daga ruwan wutar sojoji a Zamfara ne suka shigo Sokoto

Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta datse hanyoyin sadarwa a ƙananan hukumomi 14 cikin 23 dake jihar a wani mataki na daƙile ayyukan yan bindiga.

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, shine ya sanar da haka a wata fira da gidan Radiyo na VOA Hausa, ranar Litinin.

Tambuwal ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu amincewar ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, kafin ta tabbatar da datsewar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ba Ranar Maida Sabis Na Sadarwa a Jihar Zamfara, Gwamna Matawalle Ya Yi Jawabi

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal
Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnati ta datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 na jihar Sokoto Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamnan yace yankunan da lamarin zai shafa sune inda hare-haren yan bindiga ya fi ƙamari a jihar, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

Meyasa gwamnati ta ɗauki wannan matakin?

Tambuwal ya bayyana cewa bayan datse hanyoyin sadarwa a Zamfara, miyagun yan bindiga sun ƙara yawan kai harinsu a Sokoto.

Bugu da ƙari gwamnan yace matakan da aka ɗauka a Zamfara, su ne suka jawo yan ta'addan suke gudowa zuwa jihar Sokoto.

Tambuwal yace:

"Saboda nasarar da rundunar sojoji take samu kan yan bindigan a Zamfara, yasa suka fara tserowa zuwa jihar Sokoto."

Wane kananan hukumomi hanin ya shafa?

Gwamna Tambuwa yace yankunan da datse hanyoyin sadarwan ya shafa sun haɗa da Dange Shuni, Tambuwal, Sabon Birni, Raba, Tureta, Goronyo, Tangaza da kuma karamar hukumar Isa da sauransu.

Kara karanta wannan

Barin wuta ta sama: Gwamnan Yobe ya umurci asibitocin gwamnati da su kula da wadanda suka jikkata

Ƙaramar hukumar Isa ta haɗa iyaka da karamar hukumar Shinkafi dake jihar Zamfara, yayin da Goronyo da Sabon Birni suka haɗa iyaka da jamhuriyar Nijar.

A wani labarin kuma Wani Mutumi Ya Dirkawa Diyarsa Yar Shekara 19 Ciki, Yan Sanda Sun Damke Shi

Rundunar yan sanda reshen jihar Ogun, ta bayyana cewa ta damke wani mutumi da ya yi wa yarsa da ya haifa ciki.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, yace ɗiyar mutumin ce ta kawo rahoton abinda mahaifinta ya jima yana mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel