Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai

Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai

  • Wajibi ne a kula da su kuma a karamtasu a doka bayan sun mika wuya, cewar Kwamandan
  • Bin doka da tsari kawai zai iya kawo karshen wannan yaki da Boko Haram
  • Kakakin Soji yace yan ta'addan ISWAP sun fara daukan sabbin mayaka

Tiyata Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa yan Najeriya da duniya cewa za'a hukunta yan Boko Haram da suka mika wuya, ba zasu tsira daga hukuncin laifukan da suka yi ba.

A hirar da yayi da manema labarai a hedkwatar rundunar dake Maiduguri, Janar Musa yace babu wanda zai yafewa dubban yan ta'addan Boko Haram da suka aikata muggan laifuka irin wannan, rahoton Vanguard.

Yace lallai suna sane da maganganun da ake amma dokokin gidan Soja basu bada daman kashe mayakin da ya mika wuya ba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa

A cewarsa, wajibi ne karramashi da kuma bashi wajen zama.

Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai
Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai Hoto: Repentant
Asali: Twitter

A cewarsa:

"Amma yawancin mutane basu fahimci hakan ba, sai su rika cewa muna lallashinsu. Ba haka bane, kawai muna abinda ya kamata ne saboda wajibi ne a bi doka. Babu wanda zai sakesu su tafi."
"Sojoji basu da hurumin hukunta yan ta'adda, innama aikinmu gudanar da bincike da kuma mikasu ga hukumomin da suka dace don hukuntasu."

'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa

Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Najeriya, ya ce 'yan ta'addan ISWAP sun fara gagarumin gangamin diban jama'a domin zama mambobinsu.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, rundunar sojin ta kaddamar da hare-hare kan miyagun 'yan ta'addan karkashin Operation Hadin Kai a yankin arewa maso gabasa ta kasar nan.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garkuwa da wasu a Sokoto

Daruruwan 'yan ta'adda da suka hada da manyan kwamandojinsu sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a makonni kalilan da suka gabata.

A yayin zagayen rundunar Hadin Kai a Maiduguri, jihar Borno a ranar Lahadi, Nwachukwu ya yi kira ga masu yada labarai da su taimaka wurin toshe duk wata kafar yaudarar jama'a su shiga kungiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel