Yan kudu: Son kai ne Buhari ya yi sansanin sojin ruwa a Kano bai yi a Bayelsa ba

Yan kudu: Son kai ne Buhari ya yi sansanin sojin ruwa a Kano bai yi a Bayelsa ba

  • Dattijo mai fada a ji a kabilar Ijaw ya bayyana bacin ransa ga shirin gwamnatin Buhari na gina sansanin sojin ruwa a Kano
  • Ya bayyana cewa, wannan son zuciya ne karara irin na gwamnatin shugaba Buhari na fifita yankin Arewa
  • Ya bayyana haka ne cikin wata budaddiyar wasikar da gidan jaridar Punch ta wallafa ranar Litinin 20 ga watan Satumba

Dattijo kuma babban jigon kabilar Ijaw, Cif Edwin Clark, ya caccaki Babban Hafsan Sojojin Ruwa (CNS), Admiral Awwal Zubairu, kan shirin rundunar sojin ruwan Najeriya na kafa sansanin sojan ruwa a jihar Kano.

A wata budaddiyar wasika da ya aike ga CNS a ranar Litinin, 20 ga Satumba, Clark ya yi tir da amincewa da kafa sansanin sojojin ruwa a Kano, yana mai cewa matakin yana daya daga cikin ayyukan son kai da gwamnatin Buhari ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

Yan kudu: Son kai ne Buhari ya yi sansanin sojin ruwa a Kano ba ta yi Bayelsa ba
Edwin Clark, dattijon Ijaw | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wani yanki daga cikin wasikar da jaridar The Punch ta wallafa ya ce:

"Cewa ana gina sabon sansanin sojan ruwa a tsakiyar sahel wanda duk duniya ta sani a halin yanzu na fuskantar barazanar hamada da ke yaduwa cikin sauri kuma ba tare da wani la'akari ba.
"Idan har za a kafa wasu sansanonin sojan ruwa a cikin kasar, me zai hana a kafa a jihohin gabar tekun Najeriya, musamman a yankin Neja Delta inda yawancin gabar ruwan Najeriya take kuma take bukatar kariya?
“Kuna tsammanin saboda kawai kuna gudanar da gwamnati sai a ki kula da sauran 'yan Najeriya a matsayinsu na ‘yan kasa na biyu?
“Yana da wahala ma a iya rarrabewa da kuma sanin dalilin da yasa kuka yi niyyar cunkushe Arewa wacce tuni ta cika da manyan kayan aikin soji, musamman a wurare kamar jihohin Kaduna da Kano. Dole ne a sami iyaka ga son kai da son zuciya.”

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke wani sojan bogi dan shekara 28 dauke da bindiga da sauransu

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kaca-kaca da shirin gwamnatin tarayya na ciyo sabon bashi na kasashen waje, kuma ci gaba da tara bashin ta'addanci ne, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce gwamnatin Buhari na tara basussuka ne ga masu zuwa a bayanta, yana mai bayyana hakan a matsayin "ta'addanci."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gabatar da bukatar neman amincewa don karbo sabbin basussuka na kasashen waje na $4.054bn da €710m ga majalisar kasa.

Bukatar tana cikin wasikar da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta a zaman zauren majalisar.

A cikin wasikar, Buhari ya bayyana cewa saboda “bukatu masu tasowa,” akwai bukatar tara karin kudade don wasu “manyan ayyuka”.

Son hada kan Najeriya na saka ni hauka, Okorocha ya nuna damuwarsa kan Najeriya

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Rundunar soji ta kai farmaki sansanin ‘yan bindiga, ta ceto babban sojan da aka sace a NDA

A wani labarin, Rochas Okorocha, sanata mai wakiltar Imo ta yamma kuma tsohon gwamnan jihar ta Imo, ya ce hangen nesan sa na hada kan Najeriya yana saka shi ya ji kamar zai hauka.

Okorocha ya yi wannan magana ne a ranar Litinin 20 ga watan Satumba yayin wata tattaunawa da manema labarai da kungiyar 'yan jaridaN Najeriya (NUJ) reshen babban birnin tarayya (FCT).

FCT NUJ ta karbi bakuncin tsohon gwamnan na jihar Imo ne gabanin shirin murnar cikarsa shekaru 59 a duniya, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel