Son hada kan Najeriya na saka ni hauka, Okorocha ya nuna damuwarsa kan Najeriya
- Rochas Okorocha ya bayyana cewa, son hada kan Najeriya na saka shi ya ji kamar zai yi hauka
- Ya bayyana haka ne yayin da aka tambayeshi ko yana da burin tsayawa takarar shugaban kasa
- Ya kuma shawarci mata a kasar da su tsaya tsayin daka wajen neman kujerun mulki don kai kasar ga tudun mun tsira
Abuja - Rochas Okorocha, sanata mai wakiltar Imo ta yamma kuma tsohon gwamnan jihar ta Imo, ya ce hangen nesan sa na hada kan Najeriya yana saka shi ya ji kamar zai hauka.
Okorocha ya yi wannan magana ne a ranar Litinin 20 ga watan Satumba yayin wata tattaunawa da manema labarai da kungiyar 'yan jaridaN Najeriya (NUJ) reshen babban birnin tarayya (FCT).
FCT NUJ ta karbi bakuncin tsohon gwamnan na jihar Imo ne gabanin shirin murnar cikarsa shekaru 59 a duniya, The Cable ta ruwaito.
Da yake amsa tambaya kan ko zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023, Sanatan ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ba ni da burin zama shugaban kasa amma hangen nesa na samun hadin kan Najeriya na haukata ni."
Ya kamata su shiga siyasa
Sanatan ya yi kira ga mata da su yi gwagwarmayar neman mulki, inda ya jaddada cewa su ne jinsin da suka fi hankali fiye da maza.
A cewarsa:
"Mace a Afirka tana da girma amma muna daukar ta kamar ita 'yar aji na biyu ne da nufin yiwa namiji hidima amma ba su fahimci cewa mace sai da ta fara zama namiji ba kafin ta zama mace."
“Mace kari ce kan namiji; ya kamata ace an kira ta da namiji amma saboda tana daukar ciki shi yasa ake kiranta da mace.
“Suna da hangen nesa fiye da yadda muke iya hange kuma sun fi fahimta sosai. Idan duk mata suna da karfin iko kuma akwai dorewar kudi ga mata, ba za mu samu wani tashin hankali ba."
Okorocha ya shawarci mata kan cewa su zama masu jajircewa da kuma tsoma kansu cikin siyasa domin kawowa kasa ci gaba mai dorewa.
Sarki a Arewacin Najeriya ya ce mata su karbi mulki a hannun Buhari a 2023 kawai
Mai martaba Sarkin Keffi, Alhaji Shehu Yamusa III, ya yi kira ga matan Najeriya da su nuna sha’awarsu ta shugabancin kasa domin su gaji shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a shekarar 2023, yana mai cewa hakan ba zai gagara ba.
A cewarsa, ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da kabila ko alakar siyasa ba, dole ne su raba tunanin al’adu da siyasa don samar da mafi kyawun shugabanci a kasar, Punch ta ruwaito.
Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Jami'ar Jihar Nasarawa, ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis 16 ga watan Satumba.
Ya bayyana haka ne lokacin da mambobin tafiyar 'National Democratic Institute International Working Group for Supporting the Advancement of Gender Equality Programme', suka ziyarce shi a fadarsa.
Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya
A wani labarin, Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kaca-kaca da shirin gwamnatin tarayya na ciyo sabon bashi na kasashen waje, kuma ci gaba da tara bashin ta'addanci ne, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce gwamnatin Buhari na tara basussuka ne ga masu zuwa a bayanta, yana mai bayyana hakan a matsayin "ta'addanci."
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gabatar da bukatar neman amincewa don karbo sabbin basussuka na kasashen waje na $4.054bn da €710m ga majalisar kasa.
Asali: Legit.ng