Batun yankin da za a ba tikitin Shugaban kasa a 2023 ya raba kan wasu Gwamnonin PDP

Batun yankin da za a ba tikitin Shugaban kasa a 2023 ya raba kan wasu Gwamnonin PDP

  • An samu rabuwar kai a dalilin yankin da zai rike wa PDP tuta a zaben 2023
  • Wasu suna ganin ‘Dan kudu ya kamata ya yi wa PDP takarar shugaban kasa
  • ‘Yan siyasan Arewa na ganin lokacinsu ne bayan mulkin Goodluck Jonathan

Yayin da aka fara shirya wa zaben 2023, sai aka ji rahoto daga The Nation cewa wani rikici ya na neman bijiro wa jam’iyyar PDP a kan takarar shugaban kasa.

Rahoton yace an samu sabani ne a game da yankin da za a ba tutar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP daga kudancin Najeriya suna ganin bai kamata ‘dan Arewa ya sake tsaya wa takarar shugaban kasa bayan Muhammadu Buhari ba.

Sai dai a ‘yan kwanakin nan, wasu manyan jam’iyyar PDP suna yunkurin ruguza lissafin ‘yan siyasar kudancin Najeriya, ta yadda za a ba ‘dan Arewa tikiti.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Kudu ba za ta goyi bayan duk jam’iyyar da ta tsayar da dan arewa ba, in ji gwamnan APC

'Yan Kudu kadai ke neman shugaban PDP

Jaridar tace zaben shugaban jam’iyya na kasa da ake shirin yi, ya kara jawo dar-dar a PDP. Babu wani daga Arewa da yake sha’awar zama shugaban jam’iyyar.

Wasu Gwamnonin PDP
Gwamnonin PDP Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Dabarar ita ce ‘dan kudu ya zama shugaban jam’iyya ta yadda Arewa za ta samu takara a 2023.

Wasu gwamnoni kamar Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom suna gargadin ‘ya ‘yan PDP cewa idan kudu ta fito da shugaban jam’iyya, Arewa za a kai takara.

Masu ra’ayi dabam suna ganin cewa Goodluck Jonathan ne wanda yayi mulkin karshe a PDP, don haka idan za a shiga wani zaben, ya kamata a ba Arewa dama.

Menene ra'ayin gwamnonin kudancin Najeriya?

A makon jiya Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya sake jaddada cewa ba za su yarda wata jam’iyya ta ba ‘Dan Arewa tikitin shugaban kasa a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Sauya-sheka: Fani-Kayode, Matawalle da sauran ‘Yan siyasan da suka girgiza kowa da shiga APC

Bayan wani taro da aka yi, Gwamna Oluwarotimi Akeredolu yace kan duka gwamnonin kudancin kasar ya hadu a kan cewa ‘Yan kudu za a ba tuta a zabe na gaba.

Meyasa FFK ya dawo APC

A makon da ya gabata ne aka ji cewa Femi Fani-Kayode ya bar PDP, ya dawo APC. Tsohon Ministan kasar ya kare kan shi bayan komawarsa jam’iyyar APC.

Fani-Kayode yace ya rika caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a da a bisa jahilci, ya kuma ce ba don APC ta canza salo ba, da ba zai bar jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel