Sauya-sheka: Fani-Kayode, Matawalle da sauran ‘Yan siyasan da suka girgiza kowa da shiga APC
Ba bakon abu ba ne a ga ‘dan siyasa a Najeriya ya sauya-sheka daga jam’iyyarsa zuwa wanda yake adawa da ita, musamman ya tsallaka jam’iyya mai mulki.
Wannan ya sa ake zargin ‘yan siyasan kasar nan da rashin akida. ‘Dan siyasa zai iya sauya-sheka zuwa jam’iyya ko da ya yi rantsu wa cewa ba zai canza gida ba.
Legit.ng Hausa ta tattaro wasu sauye-sauyen sheka da aka yi da ya ba jama’a mamaki bayan 2019.
1. Femi Fani-Kayode
A ranar 16 ga watan Satumba, 2021, aka ga Femi Fani-Kayode tare da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa, ana yi masa wankar dawo wa APC.
Tsohon Ministan ya koma APC bayan duk sukar da ya yi wa jam’iyyar da shugaba Buhari a baya.
2. Bello Matawalle
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwanaki Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya yi watsi da jam’iyyar PDP da ta ba shi damar tsaya wa takara, har kuma ya yi nasarar zama gwamna a zaben 2019.
A watan Yuli ne fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da sauya sheƙar gwamna Bello Matawalle daga PDP zuwa APC.
3. David Umahi
Ficewar Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC) ta ba mutane da-dama mamaki sosai.
Da yake bayyana dalilinsa na sauya sheka daga jam’iyyar PDP, Umahi yace shugaban kasa ne ya jawo ra’ayinsa.
4. Ben Ayade
A watan Mayun 2021 aka ji labari gwamnan jihar Kross Ribas, Ben Ayade, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP, ya koma APC, bayan tsawon lokaci ana rade-radi.
5. Yakubu Dogara
A shekarar 2020 Hon. Yakubu Dogara ya girgiza siyasar jihar Bauchi, aka ji ya fice daga jam’iyyar PDP, ya sake koma wa APC, bayan ya sake lashe zaben majalisa.
'Kwararan Dalilan Da Suka Sa Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan Ke Jinkirin Komawa Jam’iyyar APC
A takardar murabus dinsa, tsohon shugaban majalisar wakilan ya bayyana sabaninsa da gwamna Bala Mohammed.
6. Shehu Sani
A watan Yulin shekarar nan aka ji cewa tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya fice daga jam’iyyar PRP. Ana tunanin zai koma jam’iyyar PDP ne.
Sanata Shehu Sani ya shiga PRP ne bayan ya gaza samun tikitin takara a jam’iyyar APC a 2018.
Ni na jawo wasu Gwamnoni - FFK
Da ya ke jawabi dazu da rana, Fani-Kayode yace ya taka muhimmiyar rawa wurin zawarcin gwamnonin jam'iyyar PDP da suka koma APC a kwanakin baya.
Tsohon jigon adawan yace yana daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar APC a shekarar 2013.
Asali: Legit.ng