Bayan 'yan fashin daji sun raba wasika, an tura karin 'yan sanda Sokoto

Bayan 'yan fashin daji sun raba wasika, an tura karin 'yan sanda Sokoto

  • Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tura karin jami'ai wasu yankunan da 'yan fashin daji suka aiko wa da wasika
  • Kamar yadda wasikar ta bayyana, miyagun sun ce ko daruruwan sojoji za a tura wa jama'a, ba za su ki kai farmakin ba
  • Sai dai rundunar 'yan sandan ta ce ba za ta dauka wannan al'amari da wasa ba, hakan yasa ta tura jami'ai domin jiran ko ta kwana

Sokoto - Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tura jami'ai yankunan da ake zargin miyagun 'yan fashin daji za su kai farmaki a jihar.

Premium Times ta ruwaito yadda wasu 'yan bindiga a makon da ya gabata suka raba wasika a harshen hausa inda suka sanar da yankunan shirinsu na kai musu farmaki.

Bayan 'yan fashin daji sun raba wasika, an tura karin 'yan sanda Sokoto
Bayan 'yan fashin daji sun raba wasika, an tura karin 'yan sanda Sokoto. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wasikar, 'yan bindigan sun sanar da mazauna yankin cewa, za su iya gayyatar sojoji sama da dari domin ba su kariya amma sai sun kai farmakin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sanar min salon da suke bi wurin guje wa luguden sojin sama, Gumi

Yankunan da aka lissafo sun hada da kwanar Kimba, Shuni, Dange da Rikina, Premium Times ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mai suna Basharu Altine a garin Isa, ya ce hankula sun dinga tashi a yankunan tun bayan da suka samu wasikun.

"Wasu jama'an sun yarda cewa wasikun na bogi ne kuma wasu yara ne suka rubuta amma ba za mu yi shiru ba saboda 'yan bindigan na iya yin komai," Altine ya ce.

Ya kara da cewa, wasu matasa ne suka tsinto wasikun a Kwanar Kimba waccan Asabar da ta gabata.

Ba za mu dauka wannan barazanar da sauki ba, 'Yan sanda

Amma kuma, yayin tsokaci kan lamarin, mai magana da yawun 'yan sanda na jihar, Sanusi Abubakar, ya ce 'yan sanda ba za su dauka wannan barazanar da wasa ba.

Ya ce an sake tura wasu jami'ai a wuraren da aka lissafo domin tsare su daga kowanne irin farmaki.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

"Amma idan aka duba rubutun, ba a rubuta shi da kyau ba kuma da kyar ake gane sakon. Amma mun ce wa kanmu, ba za mu yi wasa da irin wannan ba, kada ya zama gaskiya.
"A gare mu, ba mu da tabbacin barazanar ta gaskiya ce. Amma ba za mu sassauta ba kuma. Mun dauka dukkan matakan da suka dace, an kara jami'ai a yankin," yace.

'Yan bindiga sun sanar min salon da suke bi wurin guje wa luguden sojin sama, Gumi

A wani labari na daban, sanannen malamin addinin Islama mazaunin Kaduna, ya kara tabbatar wa da jama'a cewa a koda yaushe ya na samun damar tattaunawa da 'yan fashin dajin da suka addabi arewacin Najeriya.

A takardar da malamin ya fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa gungun 'yan bindiga sun sanar da shi cewa luguden ruwan wutan da sojin saman ke yi ba ya taba su, sai dai ya taba matansu da 'ya'yansu, domin kuwa suna da salon kauce musu, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun yi awon gaba da wasu da dama bayan sun yaudare su da kiran Sallah a Sokoto

Gumi ya ce 'yan bindigan sun kware tare da zama 'yan hannu wurin kauce wa duk wani bam da sojin sama za su wurgo, hakan ne yasa da kyar a iya kama su ko halaka su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel