'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garkuwa da wasu a Sokoto

'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garkuwa da wasu a Sokoto

  • Rundunar 'yan sanda Sokoto ta tabbatar da kisan rai daya tare da sace wasu mutane da yawa da miyagun 'yan bindiga suka yi
  • An gano cewa, miyagun sun shiga karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto inda suka sheke wani dan kasuwa
  • Taimakon 'yan sanda da 'yan sintiri ne yasa aka ceto yaro daya daga cikin biyar din da suka iza keyarsu

Sokoto - Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto a ranar Asabar ta tabbatar da halakar rai 1 tare da sace wasu mutane masu yawa sakamakon farmakin da wasu miyagun 'yan bindiga suka kai karamar hukumar Tangaza ta jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan, ASP Sunusi Abubakar, wanda ya tabbatar da farmakin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Sokoto, ya ce harin ya auku da yammacin Juma'a.

Kara karanta wannan

'Yan sanda za su gurfanar da wata matashiya ‘yar shekara 25 da ke yi wa ‘yan bindiga leken asiri a Katsina

'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garuwa da wasu a Sokoto
'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garuwa da wasu a Sokoto. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
"Mun samu rahoton da wasu 'yan bindiga suka kai inda suka tsinkayi hedkwatar karamar hukumar Tangaza a yammacin Juma'a.
"Yan bindigan sun sheke dan kasuwa daya, sun sace wasu mutane da har yanzu ba a san yawansu ba tare da yin awon gaba da kayan abinci da ababen sha.
"Amma kuma, 'yan sanda tare da hadin guiwar wasu jami'an tsaro suna cigaba da bincikar lamarin," yace.

Sai dai wata majiya da ta tattauna da NAN a Tangaza, ta ce wadanda ake zargin 'yan bindiga ne sun dinga harbe-harbe a iska inda suka kashe dan kasuwan a take kuma wata yarinya ta rasu bayan an kai ta asibiti.

Ya kara da cewa, wasu mutum uku sun samu miyagun raunika kuma suna karbar kulawar likitoci a asibiti, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga bisani, NAF ta dauka alhakin yi wa farar hula ruwan wuta a Yobe

"Sai dai, taimakon da jami'an tsaro suka kai tare da 'yan sintiri yasa an ceto yaro daya daga cikin biyar da 'yan bindigan suka sace," yace.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya sanar da cewa, ayyukan da jami'an tsaro ke yi a Zamfara da jihohi masu makwabtaka da ita tare da rufe manyan kasuwannin jihohin sun matukar tada hankalin 'yan bindigan.

Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya

A wani labari na daban, iyalan wadanda mummunan lamarin da ya faru a jihar Yobe da su sakamakon luguden wutan da jirgin NAF ya so yi kan 'yan ta'addan Boko Haram, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta biya su diyya.

Sun alakanta bukatarsu da dalilin cewa, gwamnati a kowanne mataki a Najeriya ba ta cika biyan diyya ba ga jama'a da aka yi wa barna, Daily Trust ta ruwaito.

Daga ciki mutum takwas da suka rasu, tsoffafi uku da wata mata wadanda suka bar kananan yara. Akwai yara kanana hudu da suka rasa rayukansu da kuma wasu gidaje da suka kone.

Kara karanta wannan

Bayan 'yan fashin daji sun raba wasika, gwamnati ta dauka matakin gaggawa a Sokoto

Asali: Legit.ng

Online view pixel