Dokar VAT za ta talauta Jihohi 30, Gwamna Wike yace sai dai sama da kasa su hade

Dokar VAT za ta talauta Jihohi 30, Gwamna Wike yace sai dai sama da kasa su hade

Jihohi da-dama a Najeriya na fuskantar kalubalen kudin tafiyar da Gwamnati

Gwamnoni 30 ba za su iya rike kansu ba idan aka kyale jihohi da alhakin VAT

Gwamnan jihar Ribas yace babu ja da baya, yace a daina biyan harajin ga FIRS

Jihohi da-dama a Najeriya ba za su iya sauke nauyin da ke kansu ba domin gwamnatin tarayya za ta rasa kaso na abin da take samu daga harajin VAT.

Baya ga hukuncin da kotu ta yi inda ta ba jihohi damar karbar harajinsu, gwamnatin Najeriya tana fama da matsalar karancin kudin-shiga a halin yanzu.

Daily Trust tace mafi yawan jihohi sun dogara ne da kason da suke samu daga asusun hadaka na FAAC saboda gwamnoninsu ba su samun kudin-shiga.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

Jihohin Ribas da Legas ne suke tattara 70% na harajin kayan masarufi a Najeriya, amma a karshe ana raba kudin ne tare da sauran gwamnonin jihohi 36.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A baya jami'an FIRS ne suke tattara VAT, sai ta raba kudin inda gwamnatin tarayya ta ke karbar 15%, jihohi su tashi da 50%, sai a ba kananan hukumomi 35%.

Gwamna Wike
Shugaban kasa Buhari da Gwamna Wike Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Binciken da jaridar tayi ya nuna cewa a halin yanzu jihohi 30 ba za su iya rike kansu ba idan abin da gwamnati take samu daga harajin VAT ya yi kasa.

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da ya shigar da kara a kotu ya dage a kan bakararsa, yace ko sama da kasa za su hade ba zai bar FIRS ta karbi harajinsu ba.

Nyesom Wike ya shaida wa kamfanoni da ‘yan kasuwan da ke Ribas su shirya biyan VAT tun daga karshen watan Satumban nan ga gwamnatin Ribas.

Kara karanta wannan

VAT: Shari’ar Gwamnatin Ribas da Gwamnatin Tarayya ya raba kan Jihohi zuwa gidaje 3

Akwai adalci a Najeriya?

“Bari in fada maku rashin adalcin da ake yi a kasar nan. A Yunin 2021, N15.1bn na VAT aka karba daga Ribas. Abin da aka bamu shi ne N4.7bn.”
“VAT din da aka karba a Kano a lokacin N2.8b ne, kuma aka ba su N2.8b. Akwai adalci kenan?

Abin da gwamnoni suke fada?

Ganin an nemi kotu ta hana FIRS ta rika tattara haraji a jihohi, an ji cewa gwamnatin Adamawa ta goyi bayan Ribas, yayin da Kogi da Gombe suke neman alfarma.

Tuni aka ji jihohin Legas da Akwa Ibom sun bayyana cewa za sua fara aiki domin a kawo kudirin da zai ba gwamnatin jiha damar tattara VAT, a maimakon FIRS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel