Dalla-dalla: Matakai 5 da zaku bi wajen cike fom na shirin 'Nigeria Jubilee Fellows'

Dalla-dalla: Matakai 5 da zaku bi wajen cike fom na shirin 'Nigeria Jubilee Fellows'

Domin rage zaman banza da kuma samar da ayyukan yi ga matasa, gwamnatin Buhari ta kirkiri shirin samar da aiki. A halin yanzu, an bude kafar yanar gizo domin fara cike fom na aikin. Hakazalika, mun tattaro muku abubuwan da ake bukata masu sha'awar neman shiga shirin ya kamata su tanada.

Gwamnatin tarayya ta bude kafar cike fom na shirin Nigeria Jubilee Fellowship, shirin da aka tsara ga matasan da suka kammala NYSC a Najeriya, Premium Times ta ruwaito.

An bude kafar a ranar Litinin 6 ga watan Satumba ga masu sha'awar cike fom kuma tsarin zai gudana na makwanni shida, "tsakanin 6 ga Satumba zuwa 20 ga Oktoba, 2021."

Gidan talabijin na Channels ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin a ranar Talatar makon jiya ya kuma bukaci matasa a Najeriya da su yi hobbasa wajen shiga shirin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Dama ta samu: Gwamnatin Buhari ta bude kafar daukar aiki ga 'yan Najeriya
Shirin Nigeria Jubilee Fellowship | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shirin hadin gwiwa ne na karfafa gwiwar matasa tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Shirin Ci gaban Majalisar Dinkin Duniya (UNDP).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shirin yana nufin hada kwararrun masu digiri ga damar aiki na cikin gida don nuna kwarewarsu na iya aiki ga ma'aikatu daban-daban da kuma horar dasu ilimi daban-daban na duniya.

A cewar shugaba Buhari:

"Ana sa ran shirin zai samar da sabbin dama ga masu digiri 20,000 a shekara yayin da masu cin gajiyar shirin za su iya inganta damar da aka ba su kuma akwai niyyar sada 'yan Najeriya da ilimin aiki da dabarun da suka dace na tsawon watanni 12, tare da ko ba tare da kwarewar aiki ba, ta yadda za a hada su da damar samun aikin yi a cikin gida."

Hakanan za a ba da zabi uku ga matasan bayan kammala shirin, wadanda suka hada da ci gaba da aiki da kungiyoyin da suka basu aiki, damar kasuwanci, da dandamali don gasa da samun damar ayyukan yi nan gaba.

Kara karanta wannan

Buhari ya kori ministocinsa: Martani da shawarin 'yan Najeriya ga shugaban kasa

Sharuddun shiga shirin

Domin cancantar shiga shirin, mai nema dole ne ya zama dan Najeriya kuma ya kammala digiri (Digiri na farko) daga kowane fannin ilimi kuma ya kammala karatu daga 2017 zuwa sama.

Masu nema dole ne su kammala karatun digiri da akalla karamin makin aji na biyu (2.2) ko sama kuma dole ne su kasance akalla 'yan shekaru 30.

Dole ne masu neman shiga shirin su kasance ba sa aiki da wata ma'aikata a halin yanzu, kuma su kasance sun kammala bautar kasa (NYSC) ko kuma sun samu takardar dage shirin NYSC a kansu.

Sauran abubuwan da ake bukata sune: masu nema dole ne su nuna sha'awa/jajircewa a cikin aikin da suka zaba sannan kuma su nuna sha'awa/jajircewa don ba da gudummawa ga ci gaban zamantakewar tattalin arzikin Najeriya.

Hakanan dole ne su sami kwarewa wajen sarrafa lokaci da nuna kwarewa kuma suna da kyawawan dabarun magana da rubutu.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hallaka dan Sanata Bala Na'Allah da aka yi

Domin samun karin bayani da kuma damar shiga shirin, za ku iya shiga shafin yanar gizo da aka tanada don shirin ta nan https://www.njfp.ng/.

Dalla-dalla yadda za ku cike form din shirin Nigeria Jubilee Fellowship

A binciken da Legit.ng ta yi a kafar yanar gizo da gwamnati ta samar don shirin, mun tattaro matakan da ake bi wajen cike fom na shirin.

Ga bayani kamar haka:

1. Sunan farko (Firstname):

Bayan bude shafin yanar gizon, masu sha'awar cike fom din dole ne su fara cike fom din ta hanyar sanya sunayensu na farko.

2. Sunan mahaifa (Surname):

Abu na gaba shine sanya sunan mahaifi, ko sunan ahali.

3. Adireshin yanar gizo na imel (Email):

Sannan, dole ne mutum ya samar da adireshin imel na musamman da ba a taba amfani dashi a kan kafar shirin

4. Kalmar sirri ta budewa (Password):

Mataki na gaba shine kirkirar kalmar sirri na budewa ga adireshin imel na musamman da aka samar.

Kara karanta wannan

NDA: Babban malamin adddini ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya, ya ce karin matsaloli na tafe

5. Tabbatar da kalmar sirri ta budewa

Mataki na karshe shine tabbatar da kalmar sirrin budewa da aka kirkira.

Bayan kammala cike fom din, za a aika sakon imel zuwa adireshin imel din da aka bayar. Idan baku samu sakon na imel ba, duba babban fayil dinku mai suna Spam/Junk watakila sakon ya fada can.

Sabon bayani: Duk wanda aka zaba a shirin N-Power ya je ya yi 'Biometric'

A wani labarin, gwamnatin tarayya, ta hannun ma’aikatar ayyukan jinkai da ci gaban zamantakewa, ta fitar da sabbin bayanai kan shirin N-Power Batch C (stream 1).

Legit.ng ta rahoto cewa bayanan da ke kan shafin yanar gizo na ma'aikatar, na nuna cewa ana bukatar duk wadanda aka zaba a shirin da su gaggauta shigar da bayanan zanen yatsun hannus (Biometric) don samun cancantar shiga matakin karshe na shirin.

Ma'aikatar ta bayyana wasu hanyoyi da ya kamata wadanda aka zaban za su bi wajen ba da bayanan nasu, wanda zai bukaci shigar da zanen yatsun hannu da aka sani da Biometric a turance.

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi: Gwamnatin Buhari Zata Samar Wa Matasa Masu Digiri 20,000 Aikin Yi Mai Tsoka

Asali: Legit.ng

Online view pixel