Buhari ya kori ministocinsa: Martani da shawarin 'yan Najeriya ga shugaban kasa

Buhari ya kori ministocinsa: Martani da shawarin 'yan Najeriya ga shugaban kasa

  • A yau Laraba 1 ga watan Satumba shugaba Buhari ya sallami wasu daga cikin ministocinsa
  • Wannan sallama ta girgiza da yawan 'yan Najeriya, lamarin da ya jawo cece-kuce a kasar
  • Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu, Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a

A wani abin da ya zama abin mamaki ga 'yan Najeriya da yawa ya kuma girgiza su, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 1 ga Satumba ya sallami wasu ministocinsa biyu daga aiki.

A cikin shekaru hudun farko da yayi akan mulki tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, shugaban ya rike dukkan membobin majalisarsa hannu bibbiyu har zuwa karshen wa'adin mulkinsa na farko.

Mutane da yawa na ganin membobin majalisar Buhari za su ci gaba da kasancewa a mukamansu har zuwa shekakar 2023 lokacin da Buhari zai bar ofis a matsayin shugaban Tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

'Yan Najeriya sun shawarci shugaba Buhari bayan ya kori ministocinsa
Shugaba Buhari a Aso Rock | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sai dai, lamari ya sha bambam, yayin da shugaban, ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Femi Adesina, ya sanar da korar ministan wutar lantarki, Engr. Sale Mamman da na ma’aikatar noma da raya karkara, Mohammed Sabo Nanono.

Ba a bayyana dalilin korar ministocin ba amma Adesina ya ce nan ba da jimawa ba za a gabatar da manyan mukamai don cike gurbin mukaman da suka dace daidai da bukatun kundin tsarin mulki.

Shugaba Buhari ya kuma lura cewa tsarin sake fasalin majalisar ministocinsa zai ci gaba bayan tafiyar ministocin biyu.

A bangare guda, 'yan Najeriya sun mayar da martani kan korar ministocin, inda suka ce matakin da shugaban ya dauka wani ci gaba ne mai kyau.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An yi gagarumin sauyi a majalisar Shugaba Buhari, an sallami ministoci 2 daga arewa

Wani mai amfani da shafin Facebook, Oguneme Romanus Uchenna, ya ce duk da shugaban ya yi abin da ya dace ta hanyar korar ministocin, amma ya kamata ya hada da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola da ministan Neja Delta, Godswill Akpabio.

Marafa Moh'd ya ce ya kamata Buhari ya sallami karin ministoci domin talakawa su samu ci gaba da cin moriyar dimokradiyya.

Ya kamata Buhari ya kara koran wasu daga cikin sauran ministocinsa

A nasa tsokacin, Hayatuddeen Tanimu ya yabawa shugaban Buhari da ya dauki matakin korar, yana mai cewa kamata dama ya sake fasalin majalisar ministocin kafin wannan lokacin.

Ya ce ya kamata a cire duk wani ministan da bai tabuka komai ba kamar yadda ya kara da cewa kamata ya yi a kori ministan tsaro saboda yanayin rashin tsaro a kasar.

Sai dai, wani kuma mai amfani da shafin Facebook, Itodo Dennis, ya ce korar ba ta da wani amfani, lura da cewa Najeriya na nutsewa cikin duhu a karkashin kulawar shugaba Buhari.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hallaka dan Sanata Bala Na'Allah da aka yi

Ashimom Timothy Msughter ya ce dole ne a kori ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige da ministan lafiya, Ehanire kan batun yajin aikin likitocin.

Ya ce Ngige ya nuna rashin biyayya ga shugaban kasa yayin da aka umurce shi da ya ajiye duk wasu abubuwan dake kasa tare da magance yajin aikin likitoci da ya ke kara ta'azzara.

'Yan APC sun roki Buhari ya mika kujerarsa zuwa kudancin Najeriya a zaben 2023

A wani labarin, wata kungiya a jam'iyyar APC mai suna South East Mandate (SEM), ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saukaka hanyoyin zabar dan takarar shugaban kasa daga amintattun mambobin jam’iyyar na Kudu maso Gabas a zaben 2023.

Ta ce manufarta ita ce tabbatar da an samu shugaba daga yankin na Kudu maso Gabas a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari, Daily Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta bukaci jam’iyyun siyasa a Najeriya da su mika tikitin takarar shugaban kasar nan zuwa Kudu maso Gabas bisa adalci, gaskiya da lamiri mai kyau.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.