Sabon bayani: Duk wanda aka zaba a shirin N-Power ya je ya yi 'Biometric'

Sabon bayani: Duk wanda aka zaba a shirin N-Power ya je ya yi 'Biometric'

  • Gwamnatin tarayya a shirin N-Power ta kara fitar da sabbin bayanai ga wadanda suka samu nasara
  • Mun samo bayanan da ke cewa, ana bukatar wadanda suka samu nasarar shiga cikin shirin da su shigar da bayanan zanen yatsun hannu
  • Mun kawo muku dalla-dalla yadda za ku shigar da bayanan kamar yadda ma'aikatar ayyukan jinkai ta wallafa

Abuja - Gwamnatin tarayya, ta hannun ma’aikatar ayyukan jinkai da ci gaban zamantakewa, ta fitar da sabbin bayanai kan shirin N-Power Batch C (stream 1).

Legit.ng ta rahoto cewa bayanan da ke kan shafin yanar gizo na ma'aikatar, https://nasims.gov.ng/, na nuna cewa ana bukatar duk wadanda aka zaba a shirin da su gaggauta shigar da bayanan zanen yatsun hannus (Biometric) don samun cancantar shiga matakin karshe na shirin.

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarnin a binciko wadanda suka kashe dan sanata

Ma'aikatar ta bayyana wasu hanyoyi da ya kamata wadanda aka zaban za su bi wajen ba da bayanan nasu, wanda zai bukaci shigar da zanen yatsun hannu da aka sani da Biometric a turance.

Sabuwar sanarwa daga N-Power: Wadanda aka zaba na Batch C za su yi 'Biometric'
Shirin N-Power | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yadda za a shigar da bayanan

Daga shafin yanar gizon ma'aikatar, mun samo wasu matakai bakwai da aka bayar domin shigar da bayanan kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

  1. Ka shiga cikin dashboard din ka sannan ka danna inda aka rubuta "verification"
  2. Danna maballin da aka rubuta "capture your fingerprint" don saukar da manhajar da za ta ba ka damar shigar da bayanan zanen yatsun hannu
  3. Bayan saukar da manhajar, shigar da bayanan da ake bukata sannan ka danna "Proceed"
  4. Ka tabbatar cewa ka hada na'urar daukar hoton zanen yatsun hannu ta biometric a jikin kwamfutarka, sannan ka danna kan "Begin Enrolment" don fara shigar da bayanan
  5. Daura yatsarka don fara shigar da bayananka
  6. Zaka shigar da zanen babban yatsar hannun dama da manuniya ta dama, sannan babban yatsar hannun hagu da manuniya ta hagu, wannan kenan ga wadanda aka zaba
  7. Bayan nasarar shigar da bayan yatsun hannu, danna "Submit" don adana bayanan

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

A cewar bayanan da muka samo, bayan nasarar shigar da bayanan, wadanda aka zaban za su iya duba shafin "verification" don tabbatar nasarar adana bayanan.

Gwamnatin Buhari ta fara kaddamar da shirin N-Power a karo na uku

A wani labarin, Gwamnatin tarayya a ranar Litinin 23 ga watan Agustan 2021 ta fara kaddamar da shirin N-Power rukunin C shashi na farko, The Nation ta ruwaito. Ma'aikatar agaji da ayyukan jin kai ta kasa ta fara aikin yin rajista na rukuni na uku na masu cin gajiyar shirin a ranar 26 ga Yuni, 2020.

Ministar agaji da ayyukan jin kai, Sadiya Farouq ta ce sama da mutum miliyan shida suka nuna sha'awarsu ga cin gajiyar shirin.

Ministar agaji da ayyukan jin kai, Sadiya Farouq ta ce sama da mutum miliyan shida suka nuna sha'awarsu ga cin gajiyar shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel