Miyetti Allah za ta tura Fulani makiyaya Amurka domin a horar dasu kiwon zamani

Miyetti Allah za ta tura Fulani makiyaya Amurka domin a horar dasu kiwon zamani

  • Kungiyar Miyetti Allah ta bayyana yunkurin horar da makiyaya yadda ake kiwon zamani
  • Wannan na zuwa ne daga bakin jakadiyar kungiyar, Amina Ajayi wacce ta halarci wani taro
  • A cewar Ajayi, shirin horarwar zai taimakawa Fulani makiyaya su kware a fannin kiwo na zamani

Nassarawa - Amina Ajayi, Jakadiyar Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hure, kungiyar raya al'adu, ta gabatar da wani shiri mai karfi na horar da Fulani makiyaya akan kiwo na zamani, wanda aka misalta shi da kwatankwacin kiwo a Amurka.

Ajayi ta bayyana hakan ne a cikin jawabinta na karbar mukami biyo bayan nada ta a matsayin Jakadiyar Miyetti Allah a hedikwatar kungiyar ta kasa da ke Uke, Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

Ta bayyana cewa rukunin farko na masu horaswa da malamai na makarantar Miyetti Allah Cattle Ranch Academy zai yi tafiya zuwa California a kasar Amurka, a farkon 2022, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore

Miyetti Allah za ta tura Fulani makiyaya Amurka domin a horar dasu kiwon zamani
Makiyaya da shanunsu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewarta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Duk da haka, kafin karshen shekarar 2021, ofishina, a karkashin kulawar Shugaban Miyetti Allah, zai shirya wani shirin horaswa na gida a Najeriya don tantancewa da daukar rukunin farko na masu horarwa da malaman da za su je Silicon Valley, California, don horon kasashen waje.
“Babban makasudin shirin shine a horar da su fasahohin zamani kuma ingantattu a fannin kiwo, wuraren kiwo da kiwo a kebabben wuri.
"Kamfanin mu na Silicon Valley Nigeria Development Development (SV-NED Inc) ya kammala dukkan shirye-shirye tare da abokan aikin mu a California, Amurka."

Za a ginawa makiyaya gidaje miliyan daya

Jakadiyar ta kuma bayyana cewa kashi na biyu na shirin ta shine gina gidaje masu rahusa miliyan daya ga Fulani makiyaya miliyan daya da ke manne da gidajen gonarsu.

Ta ce kamfanin nata ya hada gwiwa da Bankin Gidaje na Tarayya kan tsarin gidaje, ta kara da cewa shirin zai canza fuskar kasuwancin kiwo da daidaita shi da mafi kyawun ayyuka na duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Tun da farko, Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Bello Bodejo, ya yi kira ga majalisar kasa da ta kawo agaji ga makiyaya ta hanyar farfadowa da zartar da dokar Hukumar Kula da Kiwo.

Bodejo ya kuma yabawa hukumomin tsaro kan sabon kokarin da suke yi na dakile satar shanu, garkuwa da mutane, fashi da makami, da sauran ayyukan ta'addanci a kasar.

Gwamnan APC na fuskantar barazanar tsigewa kan rikicin makiyaya

Rahotannin da ke fitowa sun nuna cewa ‘yan majalisar dokokin Filato na fuskantar matsin lamba na tsige gwamna Simon Lalong kan karuwar hare -hare a jihar. An dora alhakin rikicin jihar kan karo tsakanin 'yan asalin yankin da Fulani mazauna yankin.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa mazauna jihar da suke ganin Gwamna Lalong yana da ra’ayin Fulani ne ke neman a dauki mataki akan gwamnan.

Rahoton ya bayyana cewa wasu daga cikin 'yan majalisar sun tabbatar da cewa suna fuskantar matsin lamba daga 'yan mazabarsu da suka zarge su da hadewa da gwamnan don yin watsi da su cikin rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa: Kungiyar IPOB ta tanadi makamai da bama-bamai a fadin Najeriya

Wani dan majalisar da baya son a ambaci sunansa ya bayyana cewa har yanzu majalisar bata yanke shawara kan ko za a fara shirin tsige gwamnan ba ko a’a.

Ya ce majalisar za ta yanke hukunci idan gwamnan ya gaza magance matsalolin tsaro da ke damun jihar cikin makwanni biyu.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Philip Dasun, shugaban kwamitin majalisar kan bayanai ya shaidawa manema labarai a Jos cewa yan majalisan sun himmatu wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya a jihar.

Rikici ya barke tsakanin Hausawa 'yan kasuwa da Fulani makiyaya a jihar Delta

A wani labarin, rikici ya barke a yankin Sapele, Karamar Hukumar Sapele ta jihar Delta yayin da ‘yan kasuwa Hausawa da Fulani makiyaya a yankin a ranar Litinin suka yi artabu da kare-jini-biri-jini a Kasuwar Hausa da ke kan hanyar Benin zuwa Warri, Amukpe, a cikin birni.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun roki Buhari ya mika kujerarsa zuwa kudancin Najeriya a zaben 2023

Wadanda suka shaida lamarin sun ce akalla mutane goma ne suka samu munanan raunuka a cikin farmakin da ya biyo baya sannan aka garzaya da su asibitoci daban-daban a yankin, in ji rahoton Daily Report Nigeria.

Punch ta ruwaito cewa, an lalata shagunan katako, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa yayin da wasu masu ababen hawa suke tsere suka bar ababen hawansu domin tsira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel