Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore

Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore

  • Mutuwar Olajide Sowore ta mamaye kanun labarai a cikin awannin da suka gabata bayan da wasu da ake zargin makiyaya ne suka harbe shi
  • An kashe Olajide wanda kani ne ga tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore a jihar Edo
  • Karamin Ministan Kwadago da Aiki, Festus Keyamo, ya ce zai matsa wa hukumomin tsaro don ganowa da hukunta wadanda suka kashe Olajide

FCT, Abuja - Karamin Ministan Kwadago da Aiki, Festus Keyamo (SAN), ya ce shi da sauran ‘yan kasa za su matsa wa jami’an tsaro don bin sawun wadanda suka kashe Olajide Sowore, kanin tsohon dan takarar shugaban kasa kuma dan raijin kare hakkin dan adam, Omoyele. Sowore.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Keyamo ya bayyana hakan ne a cikin wasiƙar ta'aziyya zuwa ga Sowore a ranar Asabar, 4 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore
Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore Hoto: Festus Keyamo
Asali: Facebook

A cikin wasikar ta’aziyyarsa, Keyamo ya bukaci tsohon dan takarar shugaban kasar da ya kara azama da kuma dagewa wajen taimakawa Najeriya wajen samo bakin zaren warware kalubalen da kasar ke fuskanta.

Ya rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Abin baƙin ciki ne da kaico ne cewa miyagu sun datsewa irin wannan saurayi rayuwar shi a cikin shekarunsa ta kuruciya.
"Ni da sauran 'yan kasa za mu matsa wa jami'an tsaro don bin diddigin wadannan makasan ba tare da bata lokaci ba kuma su gurfanar da su a gaban shari'a. Ya zama dole a binciki wadannan, da wasu da yawa a duk faɗin ƙasar.
"Ina roƙonku da ku yi ƙarfin hali sannan ku kasance masu himma don taimakawa al'umma su sami mafita mai ɗorewa ga wasu daga cikin waɗannan ƙalubalen."

A cewar mai fafutukar, an harbe Olajide a kan hanyarsa daga Jami'ar Igbinedion da ke jihar Edo inda yake karatun hada magunguna.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Ya ce maharan sun kasance makiyaya da masu garkuwa da mutane.

'Yan sanda sun tabbatar da kashe dan uwan Sowore

A baya mun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta tabbatar da kisan Felix Olajide Sowore, kanin mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

Jaridar The Nation ta ruwaito Sowore, a wani sako da safiyar ranar Asabar, ya ce wasu da ake zargin makiyaya / masu garkuwa da mutane ne sun kashe dan uwansa a jihar Edo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Edo, Kontongs Bello, ya ce masu garkuwa da mutane sun kashe Olajide da misalin karfe 6:00 na safiyar Asabar, jaridar ta kuma ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng