Fadar shugaban kasa: Kungiyar IPOB ta tanadi makamai da bama-bamai a fadin Najeriya

Fadar shugaban kasa: Kungiyar IPOB ta tanadi makamai da bama-bamai a fadin Najeriya

  • Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan rahoton da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fitar kwanan nan dangane da rikicin yankin kudu maso gabas
  • Da yake zargin kungiyar da daukar nauyin ‘yan ta’adda, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya ce IPOB ta tanadi makamai da bama-bamai a fadin kasar
  • Shehu ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yaki da ta’addanci kuma za ta yi watsi da “hargagin” kungiyar ta kasa da kasa

Fadar shugaban kasa a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, ta bayyana cewa haramtacciyar kungiyar nan da ke neman kafa kasar Biyafara (IPOB) ta tara tarin makamai da bama-bamai a duk fadin kasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken ‘Why Amnesty’s Entreaties Should Be Ignored, By Presidency’.

Kara karanta wannan

2023: Kada ku bari Atiku ya yi maku asarar tikitinku, kungiya ta gargadi PDP

Fadar shugaban kasa: Kungiyar IPOB ta tanadi makamai da bama-bamai a fadin Najeriya
Fadar shugaban kasa ta caccaki Amnesty International kan goyon bayan IPOB Hoto: Buhari Salau
Asali: UGC

Sanarwar ta mayar da martani ne ga rahoton karshe na kuniyar Amnesty International kan yadda hukumomin tsaro ke magance matsalar IPOB a yankin Kudu maso Gabas.

Amnesty International na buga siyasa - Garba Shehu

Garba ya ce duk da ''shelar'' Amnesty na kin nuna son kai, kungiyar na taka rawar siyasar cikin gida ne kawai a Najeriya.

Ya kara da cewa ana amfani da kungiyar mai zaman kanta na kasa da kasa a matsayin mafaka ga shugabannin kungiyar na gida don biyan bukatun kansu, yana mai cewa:

“Wannan ba sabon abu bane a Afirka. Babu wani aibu a matsayar mai fafutuka; akwai ikirarin kasancewa tsaka-tsaki, lokacin da duk hujjoji ke nuna akasin haka."

Hadimin shugaban kasar ya kara da ikirarin cewa Amnesty International ba ta da ikon zama a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kada ku bankawa Najeriya wuta da kalaman kiyayya, FG ta gargadi shugabanni

FG za ta yi watsi da ''hargagin'' Amnesty International

Shehu ya kuma ce "gwamnatin Najeriya za ta yaki ta'addanci da dukkan hanyoyin da take da su."

Ya kara da cewa:

"Za mu yi watsi da hargagin Amnesty, musamman idan ta fito daga wata kungiya da ba ta rike kanta da mizanin da ta ke bukata wasu su dauke ta ba."

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce kungiyar ta yanke shawarar "mara wa 'yan ta'adda baya, kafin 'yancin wadanda suka jikkata, da raba su da muhallansu da kisan kai", Nigerian Tribune ta ruwaito.

Sanarwar ta ce:

“IPOB na kashe ‘yan Najeriya. Suna kashe jami’an ‘yan sanda da jami’an soji tare da kona kadarorin gwamnati. Yanzu, sun tara tarin makamai da bama -bamai a duk faɗin ƙasar.”

A cikin wani rahoto da Amnesty International ta fitar, ta ce akalla mutane 115 jami'an tsaro suka kashe a cikin watanni hudu a kudu maso gabashin kasar.

Kara karanta wannan

Raba-gari: A karshe Shugaba Buhari ya bayyana wadanda ke daukar nauyin IPOB

Kungiyar ta zargi jami’an tsaro da take hakkin dan adam da aikata laifuka karkashin dokokin kasa da kasa a jihohin Anambra, Imo, Ebonyi da Abia.

A wani labari na daban, 'Yan majalisar dokokin jihar Nasarawa uku sun tsallake rijiya da baya a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, inda suka tsere daga wani "yunƙuri na kashe su" a kan babbar hanyar Akwanga zuwa Lafiya.

Jaridar Newswirengr ta kuma ruwaito cewa ‘yan majalisar wadanda suka hada da Hon Samuel Tsebe (APC-Akwanga ta Kudu), Hon David Maiyaki (APC- Karu / Gitata) da Hon Peter Akwanga (PDP- Obi 1), suna kan hanyarsu ta zuwa jana’iza ne lokacin da lamarin ya afku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng