NDLEA ta cafke dan bautar kasa da ke safarar alawa mai bugarwa daga UK
- Hukumar NDLEA ta kame alawan da aka yi da miyagun kwayoyi a babban birnin tarayya Abuja
- NDEA ta ce an kame kayan ne yayin da aka gano an shigo dasu ne tun daga kasar Burtaniya
- Hakazalika, a wasu bangarori an kame wasu kayan laifin da za a fitar zuwa kasashen waje
Abuja - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta ce ta cafke wani dan bautar kasa mai shekaru 22, Arnold Maniru, bisa zargin shigo da kilo hudu na muggan kwayoyi daga Burtaniya, Punch ta ruwaito.
Daraktan yada labarai na hukumar NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka bayar ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi 5 ga watan Satumba a Abuja.
Babafemi ya ce an kama dan bautar, wanda ke aiki tare da wata hukumar gwamnati a Abuja, a ranar Asabar, 28 ga watan Agusta, bayan da aka kame wani kaya a dakin ajiya na wani kamfanin sufuri.
Ya ce daga baya an aiwatar da isar da fakitin, wanda ke dauke da alawa da aka likawa alama da arizona an kuma samu wani babban nau'in tabar wiwi da migayun magunguna na ruwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakanan, jami'an da ke aiki da kamfanonin sufuri da sakonni a Legas sun kama kilo 1.2 na wiwi, wanda aka boye a cikin biskit da nufin fita dasu zuwa Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa.
Babafemi ya ce an kuma kame giram 920 na hodar Iblis da aka boye cikin gashin roba ake shirin tafiya dasu zuwa Saudi Arabiya daga jihar Legas.
Hukumar kwastam ta mika gurbattun magunguna na miliyoyi da ta kwata ga NAFDAC
Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta, ta karbi kayayyakin magunguna marasa rajista da darajarsu ta kai Naira miliyan 100 da Hukumar Kwastan ta kama.
Kwanturola a sashin B na sashin ayyukan kwastam na tarayya, Al-Bashir Hamisu ne ya mika kayayyakin ga NAFDAC a Kaduna, Daily Nigerian ta ruwaito.
Mista Hamisu ya ce rukunin masu sintiri na kan iyakokin kwastam sun kwace kayayyakin magungunan ne a watan Agusta.
NDLEA Ta Kwamushe Wata Mata da Hodar Iblis 100 Kunshe Cikin Al'aurarta
A wani labarin, Jami'an hukumar NDLEA sun cafke wata 'yar Najeriya da ke zaune a kasar Brazil, Misis Anita Ugochinyere Ogbonna, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe (NAIA) dake Abuja, dauke da kwalayen hodar iblis 100 da ta boye a al'aurarta da jakarta.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fada a ranar Lahadi a Abuja cewa an kama matar mai 'ya'ya uku ne a daren Juma’a lokacin da suka isa Abuja ta jirgin Qatar Air daga Sao Paulo na Brazil ta Doha babban birnin kasar Qatar.
A cewarsa, yayin binciken kwakwaf, an ciro hodar iblis 12 da ta saka a al'aurarta yayin da aka gano wasu kunshi 88 da aka saka a cikin safa a boye cikin jakarta, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng