Jami'an kwastam sun kame fatun Jakuna da ake kokarin fitar wa kasar waje

Jami'an kwastam sun kame fatun Jakuna da ake kokarin fitar wa kasar waje

  • Rundunar kwastam a jihar Legas ta cafke wasu haramtattun kayyyaki a wani dakin ajiya
  • An ruwaito cewa, an gano fatun jakuna, gawayi da guma-guman itace yayin kai farmakin
  • A halin yanzu rundunar ta ce tana kan binciken mutanen da ke da hannu a wannan kaya

Legas - Kwanturola janar na rundunar kwastam ta Najeriya, Zone A, a jiya Laraba 1 ga watan Satumba ya ce sun kame fatun jakuna masu guba, wasu fatun daban, gawayi da guma-guman itace da aka tanada don fita da su waje da dajararsu ta kai Naira biliyan 643 a jihar Legas.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, an adana kayayyakin ne da aka kama a cikin wani dakin ajiya da ke Apapa, kuma ana gab da fitar dasu tasha don cillawa da su waje lokacin da aka kama su.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Jami'an kwastam sun kame fatun Jakuna da ake kokarin fitar wa kasar waje
Jami'an hukumar kwastam | Hoto:dailynigerian.com
Asali: UGC

Da yake bayyana kamun a tashar fitar da kaya ta Kwastam ta Najeriya, da ke Ikorodu, Controller na rundunar, Ahmadu Shuaibu, ya ce an gano kayayyakin ne kusa da tashar jiragen ruwa ta Apapa kuma masu kayan sun tsere yayin da suka ga tawagar kwastam.

Shuaibu ya bayyana cewa, kadan ya hana a fitar da kayan ba dan jami'an kwastam sun kai farmakin da wajen ajiyar ba.

Ya ce ana ci gaba da kokarin ganin an gurfanar da duk wadanda ke da hannu wajen wannan aika-aika.

Manufar gwamanti na hana fitar da irin wadanann kayayyakin

A cewar Tribune Nigeria, kwanturolan ya ce ka’idar hana fitar da kaya ta yi daidai da manufofin gwamnatin tarayya na kare jinsunan da ke cikin hadari, da kare tattalin arzikin cikin gida.

Kara karanta wannan

Kada ku bankawa Najeriya wuta da kalaman kiyayya, FG ta gargadi shugabanni

Hakazalika ana nufin inganta manufar gandun daji na kasa da Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da shi, wanda a cewarsa, ana zaton hakan ya taimaka wa ci gaba mai dorewa na kasar game da kare dimbin albarkatun gandun dajin daga fitinar karewa.

Da yake mayar da martani kan yunkurin da ake zargin masu fasa-kauri na yi na samun kudin shiga a watan da ya gabata don mamaye kasuwannin kasar da abubuwan fasa kauri, Shuiabu ya ce an tura karin jami'ai don tsaron iyakokin ruwan kasar da na kasa.

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Laraba 1 ga watan Satumba ta gabatar da mutane 12 da ake zargi ciki har da tubabbun 'yan bindiga guda uku bisa laifuka daban-daban da suka hada da fashi, satar shanu da garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Ba zan cigaba da lamuntar ta'addanci ba, Lalong ga shugabannin Jos

Tubabbun 'yan bindigan su ne Abdullahi Mai-Rafi mai shekaru 43; Abbas Haruna mai shekaru 34; da Usman Hassan mai shekaru 50, jaridar Punch ta ruwaito.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Katsina, cewa ana zargin mutanen uku sun kai hari kan wani makiyayi, Alhaji Gide Suleiman, a ranar 11 ga Agusta, 2021, a dajin Dammarke a karamar hukumar Ingawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel