NDLEA Ta Kwamushe Wata Mata da Hodar Iblis 100 Kunshe Cikin Al'aurarta

NDLEA Ta Kwamushe Wata Mata da Hodar Iblis 100 Kunshe Cikin Al'aurarta

  • Jami'an hukumar NDLEA ta cafke wata mata da ta shigo Najeriya daga kasar Brazil da hudar iblis
  • An ce ta boye maganin din cikin al'aurarta da kuma jakarta, inda jami'ai suka yi ram da ita
  • Ta amsa laifinta, ta kuma bayyana dalilin da yasa ta aikata wannan mummunan aiki na safarar kwaya

Jami'an hukumar NDLEA sun cafke wata 'yar Najeriya da ke zaune a kasar Brazil, Misis Anita Ugochinyere Ogbonna, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe (NAIA) dake Abuja, dauke da kwalayen hodar iblis 100 da ta boye a al'aurarta da jakarta.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fada a ranar Lahadi a Abuja cewa an kama matar mai 'ya'ya uku ne a daren Juma’a lokacin da suka isa Abuja ta jirgin Qatar Air daga Sao Paulo na Brazil ta Doha babban birnin kasar Qatar.

A cewarsa, yayin binciken kwakwaf, an ciro hodar iblis 12 da ta saka a al'aurarta yayin da aka gano wasu kunshi 88 da aka saka a cikin safa a boye cikin jakarta, Daily Trust ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: 'Yan Sanda Sun Ceto Jariri Dan Wata Goma da 'Yar Aikin Gida Ta Sace

NDLEA Ta Kwamushe Wata Mata Dauke da Hodar Iblis 100 Kunshe Cikin Al'aurarta
Anita Ugochinyere Ogbonna | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya bayyana cewa:

“A lokacin da ake yi mata tambayoyi, Misis Ogbonna, wacce uwa ce ga 'ya’ya uku, dukkansu mazauna Brazil, ta yi ikirarin cewa ta rasa mijinta shekaru uku da suka gabata.
“Ta yi ikirarin cewa ta yanke shawarar safarar hodar iblis ne don ta samu kudi don binne mahaifinta wanda aka shirya a ranar 22 ga watan Yuli a jihar Imo.
“Ta ce wani mai suna Emeka, wanda aka fi sani da KC dake zaune a Brazil ne ya ba ta hodar don ta kawo a Najeriya a kan farashin $3,000.
“Ta ce ta tura hodar iblis din ne cikin al’aurarta bayan kokarin da ta yi na hadiyesu ya gagara.

Babafemi ya kara da cewa:

"Wacce ake zargin dake da shago inda take sayar da kayan abinci na Afirka a Brazil, ta kara da cewa sai da ta ajiye kananan yaranta uku tare da wata 'yar Kenya wacce makwabciyarta ce a Brazil kafin ta fara tafiyar-samun kudi-cikin-sauri."

Da yake mayar da martani ga nasarar da aka samu, shugaban NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai ritaya) ya yaba wa jami’an filin jirgin sama na Abuja bisa ba da goyon baya a yaki da miyagun kwayoyi, The Guardian ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Cikakken Bayani: Yadda Tankar Gas Ta Fadi a Kasuwa, Ta Yi Kaca-Kaca da Mutane 10

NDLEA ta kame wasu 'yan kasuwa 2 dauke da hodar iblis kilogram 3

A wani labarin, Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wani dan kasuwa a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe (NAIA), Abuja da wani mutum a filin jirgin saman Murtala Mohammed (MMIA), Lagos, ‘tare da hodar iblis mai nauyin kilogram uku.’

Mai magana da yawun hukumar, Mista Jonah Achema, ya fada a ranar Alhamis a Abuja cewa yayin da “aka kama Adeleke Kazeem Biola a filin jirgin saman Legas tare da kilogram 1.5 na hodar iblis a ranar Laraba, 3 ga Fabrairu 2021 a yayin tantance fasinjoji a jirgin Emirate zuwa Dubai.

"Wani dan kasuwa mazaunin Legas, Onu Oluchukwu Juma’a, an kama shi da kilogram 1.527 na miyagun kwayoyi a filin jirgin saman Abuja.” Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel