Sojin Najeriya sun yi ram da 'yan bindiga 81, sun ceto mutum 33 a arewa maso yamma , DHQ

Sojin Najeriya sun yi ram da 'yan bindiga 81, sun ceto mutum 33 a arewa maso yamma , DHQ

  • Tun bayan rabuwar kawunan ‘yan ta’addan arewa maso yammacin Najeriya, an yi ta rasa rayukan 'yan ta'addan yankin
  • Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, fiye da sojoji 25 sun rasa rayukansu sannan fiye da mayakan ISWAP 40 sun rasa rayukansu
  • Cikin makonni 3 da suka gabata hedkwatar tsaro ta ce OPHD ta kama fiye da 81 tare da masu makamantan laifuka a yankin

Arewa maso yamma - Turnukun da ya barke tsakanin mayakan ISWAP da sojoji ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama ciki har da sojoji 25 da ‘yan ta’adda 40 a yankin arewa maso gabacin Najeriya.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, tun bayan rabuwar kan ‘yan ta’addan inda suka rabu gida biyu, da bangaren shugaban da na mataimakinsa an dinga samun nasara.

Sojin Najeriya sun yi ram da 'yan bindiga 81, sun ceto mutum 33 a arewa maso yamma , DHQ
Sojin Najeriya masu yaki da 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Hedkwatar tsaro ta ce rundunar Operation Hadarin Daji ta kama fiye da ‘yan ta’adda 81 da sauran masu laifuka a cikin makwanni 3 a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan ta'addan ISWAP a Borno, sun kashe 6

Mukaddashin darektan na harkar yada labaran soji, Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan yayin da ya ke bayar da bayanai a kan ayyukan soji na kasar nan a ranar Alhamis a Abuja.

Onyeuko ya ce, sun samu nasarar ceto mutane 33 daga masu garkuwa da mutane sannan sun hallaka ‘yan bindiga fiye da 15 a cikin wannan lokacin.

Ya kara da bayyana yadda suka ragargaje ‘yan fashi da makamai guda 2 da mutane 13 da suke bayar da bayanai gare su, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

A cewarsa, rundunonin sun ragargaji ‘yan ta’adda da dama a jihar Zamfara, Katsina da jihar Sokoto.

Ya kara da cewa, rundunar Operation Safe Heaven ta kama mutane 20 da ake zargin suna da hannu a hallaka matafiya 26 a garin Rukuba a karamar hukumar Jos ta arewa da ke jihar Filato a ranar 14 ga watan Augusta.

Kara karanta wannan

Benue: Masu ruwa da tsaki na APC sun nemi Buhari ya ayyana dokar ta baci

Ya ce tuni suka tura wadanda suke zargin zuwa kotu don a yanke musu hukuncin da ya dace da su.

A cewar Onyeuko, Shugaban rundunar sojin kasa, Lucky Irabor ya kai ziyara har Jos don kwantar da tarzomar tare da samar da zaman lafiya.

Tsaro: Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansani a jihar Kano

A wani labari na daban, Shugaban rundunar sojin ruwa, Awwal Zubairu-Gambo ya yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa bayar da filin da za a gina sansanin sojin ruwa a jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Zubairu-Gambo ya yi wannan godiyar ne yayin da ya kai ziyara ga Gwamna Abdullahi Ganduje a gidan gwamnati da ke Kano a ranar Laraba.

A cewarsa, sojojin ruwan Najeriya sun gudanar da binciken lafiya a jihar don shirya wurin da aka basu don fara ayyuka. Ya kara da cewa sun amince da gina sansanoninsu a jihar Imo da jihar Legas.

Kara karanta wannan

Kar 'yan Najeriya su tsorata da yawan 'yan Boko Haram da ke tuba, CDS Irabor

Asali: Legit.ng

Online view pixel