Benue: Masu ruwa da tsaki na APC sun nemi Buhari ya ayyana dokar ta baci
- Masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar APC sun yi imanin cewa ayyana dokar ta-baci na daya daga cikin hanyoyin magance barazanar rashin tsaro a Benue
- Mambobin jam’iyya mai mulki sun yi wannan kiran ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, a Abuja
- Sanata George Akume, ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci ya bayyana hakan bayan tantance halin da ake ciki
Abuja - Mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Benue sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta ayyana dokar ta -baci don magance tabarbarewar tsaro a jihar.
Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnatoci, Sanata George Akume, yayi wannan kiran a madadin dattawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyya mai mulki yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta a Abuja, jaridar The Nation ta ruwaito.
Akume ya bayyana cewa sun yi kiran ne saboda ikirarin da Gwamna Samuel Ortom ke yi na cewa matsalar tsaro a jihar ta tabarbare ta yadda rayuwar mutane ke cikin hatsari.
A wani rahoton Vanguard, ministan wanda ke tare da Abba Moro, shugaban APC, tsoffin wakilan majalisun tarayya da na jihohi da jiga -jigan jam'iyyar yace kiran ya biyo bayan tantance halin da ake ciki.
Ya ce:
“Tun da Gwamna Ortom yana yawan zargin cewa matsalar tsaro a jihar Benuwe ta tabarbare ta yadda rayukan mutanen Benue ke cikin hatsari, muna kira ga Shugaban kasa a matsayin babban kwamandan rundunonin soji ya ayyana dokar ta-baci a jihar Benue don kawo karshen matsalar tsaro a jihar."
Akume ya roki EFCC ta yi ram da gwamnan Benue Ortom ta bincikeshi kan wasu kudi
A wani labarin, ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci, Sanata George Akume, ya nemi hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su binciki Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, Daily Trust ta ruwaito.
Akume, tsohon gwamnan jihar Benue, ya yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin 30 ga watan Agusta.
Ya kuma nemi Ortom da ya daina fadan bakaken maganganu kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng