Tsaro: Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansani a jihar Kano

Tsaro: Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansani a jihar Kano

  • Shugaban rundunar sojin ruwa, Awwal Zubairu-Gambo ya yaba wa gwamnatin jihar Kano a kan samar da filin da za a gina sansanin sojin ruwa a jihar
  • Zubairu-Gambo ya yi godiyar ne bayan ya kai wa gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ziyara a gidan gwamnatin jihar a ranar Laraba
  • A cewar sa, samar da sansanoninsu zai taimaka wurin dunkule dukkan rundunonin soji wuri guda don Najeriya ta zama tsintsiya madauri daya

Kano - Shugaban rundunar sojin ruwa, Awwal Zubairu-Gambo ya yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa bayar da filin da za a gina sansanin sojin ruwa a jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Zubairu-Gambo ya yi wannan godiyar ne yayin da ya kai ziyara ga Gwamna Abdullahi Ganduje a gidan gwamnati da ke Kano a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Musulunci Ya Haramta: Ban Goyon Bayan Halasta Amfani Da Wiwi, Ƴan Majalisar Kano Ma Basu Goyon Baya, Ganduje

Tsaro: Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansani a jihar Kano
Shugaban rundunar sojin ruwa, Zaubairu Gambo tare da Gwamna Abdullahi Ganduje. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewarsa, sojojin ruwan Najeriya sun gudanar da binciken lafiya a jihar don shirya wurin da aka basu don fara ayyuka.

Ya kara da cewa sun amince da gina sansanoninsu a jihar Imo da jihar Legas.

Kuma hakan zai taimaka wurin kara wa sojojin ruwa kwarin guiwa da kuma hade kan sojojin Najeriya, Daily Nigerian ta wallafa hakan.

Ganduje ya ce gina sansaninsu da kuma karbar masaukin shugaban rundunar sojin ruwa a jihar, alama ce da ke nuna zaman lafiyan da ke jihar.

“Mun gode da kuka amince da zaman lafiyan da ke jihar Kano. Akwai hadin kai mai yawa tsakanin jami’an tsaron da ke aiki a jihar.
“Gina sansanin rundunar sojin ruwa a Kano wata hanya ce ta samar da tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ba DSS umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin gwamnati ba

“Duk lokacin da muke da taro za mu dinga gayyatar sojin ruwa suna taimaka mana wurin samar da tsaro a jihar,” a cewar sa.

Akwai yuwuwar 'yan bindigan da suka addabi arewa maso yamma ba 'yan kasa bane, Malamin Kirista

A ranar Litinin, Bishop Martin Uzukwuo, wani babban Bishop da ke Minna ya lura da cewa yawancin ‘yan ta’addan da suke addabar Najeriya ‘yan kasar waje ne.

Uzukwuo ya bayyana hakan ne a wata hira da NAN tayi dashi a Minna, Daily Nigerian ta wallafa.

A cewarsa ya kamata gwamnatin tarayya ta kwashe duk wadanda suke da alhakin addabar kasar nan ta mayar da su kasashensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel