Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi masu tada kayar baya a Najeriya cewa su shiga taitayinsu
  • Ya bayyana karara cewa, gwamnatinsa za ta yi maganin masu kai hare-hare kan jama'a a jihar Filato
  • Ya kuma bayyana gaskiyar cewa, masu fafutukar ta'addanci basu da alaka da addini, kawai neman kudi suke

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an hukunta duk mutanen da aka samu da hannu dangane da hare-haren da aka kai kwanan nan a jihar Filato, The Cable ta ruwaito.

An kai hare-hare kan mutane da dama a garin Jos, babban birnin jihar Filato, da sauran sassan kasar a cikin ‘yan kwanakin nan, wanda ya yi sanadiyar kashe-kashen mutane da dama, yayin da wasu mazauna garin da dama suka samu raunuka.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka rabawa mabukata kayan garan matar Yusuf Buhari, Zahra Bayero

Sakamakon hare-haren da aka kai a Jos wasu gwamnatocin jihohi sun kwashe 'yan asalin jihohinsu dake karatu daga jihar ta Filato.

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos
Shugaban kasa Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar a ranar Lahadin 29 ga watan Agusta, Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya, su hada kai don yaki da tashe-tashen hankula.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

In ji rahoton Ripples Nigeria, shugaban ya gargadi shugabannin addinai da na al'umma kan tunzura mabiyansu zuwa fadawa tashin hankali, sannan ya yi gargadi game da yada gurbatattun labarai kan kalubalen tsaro a kasar.

Wani yankin sanarwar ya ce:

"Fadar shugaban kasa tana son tabbatar wa dukkan 'yan kasa cewa a matsayinta na gwamnati, tana kan gaba kuma tana ci gaba da kokari don murkushe wadanda suka haddasa rikicin baya-bayan nan a jihar Filato."

Kara karanta wannan

Rikicin Jos: Jihar Kaduna ta kwashe dalibai 'yan jiharta dake karatu a jihar Filato

"Amma don samun nasara, al'ummomin mu dole ne su hada kai don yakar wadannan munanan hare-hare. Rikicin ramuwar gayya ba shine mafita ba.
“Yayin da ake kara karfafa wadannan al’ummomin da ke cikin tashin hankali da jami’an tsaro, dole ne shugabannin addinanmu, na gargajiya, da sauran shugabannin al’umma su guje ba da damar amfani da wurarensu don yada tashin hankali da tunzura tashin hankali.

Rikici bai da alaka da addini, neman kudi ne kawai

A bangare guda, shugaba Buhari ya koka kan yadda aka sauya tunanin mutane kan dangantar tashen-tashen hankulan Boko Haram, ISWAP da garkuwa da mutane da lamarin addini.

A cewar shugaba Buhari, dukkan wadannan masu aikata laifi suna yi ne saboda kudi, kuma ya kamata a hada hannu wajen kawo karshen matsalolin.

IPOB ba masu neman 'yancin kai bane

Da yake magana game da 'yan awaren IPOB, shugaba Buhari ya bayyana cewa, kungiyar na fafutuka ne saboda kudi tare da shugabanninsu dake yaudarar kasashen waje da sunan suna kare kiristocin Najeriya ne.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

A cewarsa:

“Sannan, a can yankin kudu maso gabas, IPOB ba suna fafutukar neman 'yanci bane lokacin da suke kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda da kadarorin gwamnati, kawai suna aikata ayyukan ta’addanci ne don satar kudi."

Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

A wani labarin, Sama da dalibai 70 'yan bindiaga suka sako na makarantar Islamiyya da ke garin Tegina wadanda aka yi garkuwa da su kwanaki 88 da suka gabata, PR Nigeria ta ruwaito.

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an sace daliban ne a harabar makarantar Islamiyyar dake Tegina a watan Yunin 2021.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar PRNigeria cewa daliban na kan hanyarsu ta zuwa Minna akan hanyar Kagara daga Birnin Gwari. An tsare daliban Islamiyyar na tsawon kwanaki 88 da awanni 11 gwargwadon lokacin da suka shafe a hannun 'yan bindigan kenan.

Kara karanta wannan

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Asali: Legit.ng

Online view pixel