Bidiyon yadda aka rabawa mabukata kayan garan matar Yusuf Buhari, Zahra Bayero

Bidiyon yadda aka rabawa mabukata kayan garan matar Yusuf Buhari, Zahra Bayero

  • Iyalan Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun gwangwaje wasu mabukata inda suka sanya farin ciki a zukatansu
  • An dai rabawa mutanen damin kayyakin abinci da aka kawo a matsayin gara daga masarautar Bichi zuwa ga ahlin Shugaban kasar
  • Mutane sun tofa albarkacin bakunansu a kan wannan mataki da iyalan Shugaban kasar suka dauka ta hanyar yaba masu

Makon da ya gabata ne dai aka kulla aure tsakanin dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf da diyar Sarkin Bichi, Zahra Bayero.

Bikin ya dauki hankalin mutane a fadin kasar kama daga shagulgulan da aka sha har zuwa irin tarin manyan mutanen da suka halarci daurin auren.

Bidiyon yadda aka rabawa mabukata kayan garan matar Yusuf Buhari, Zahra Bayero
Bidiyon yadda aka rabawa mabukata kayan garan matar Yusuf Buhari, Zahra Bayero Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Bisa ga al’adan mallam Bahaushe, iyalan amarya kan kai ta kayan gara wanda ake rabawa a tsakanin yan uwan angon.

Wannan yasa masarautar Bichi ta yi rawar gani wajen raka amarya Zahra da damin kayan abinci kama daga shinkafa, taliya, madara, kayan makulashe da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Har yaran masu kudi muna kamawa, Shugaban hukumar Hisbah

Sai dai mutane sun ta tofa albarkacin bakunansu kan wannan kaya da aka raka amarya da shi, inda wasu suka yi korafin cewa yayi yawa yayin da wasu suka bayar da shawarar cewa a rabawa mabukata domin idan ba haka zai baci.

A karshe dai iyalan Shugaban kasar suka yanke shawara inda suka rabawa mabukata da marasa gata.

A wani bidiyo da shafin surukan shugaban kasar mai suna keepingupwiththeindimis ya wallafa a Instagram ya nuno yadda mabukata suka yi dogon layi yayin da ake raba masu kayayyakin cikin wata leda da ke dauke da sunan amarya Zahra da angonta Yusuf.

Hakan ya burge wasu mutane da dama a shafin inda suka tofa nasu

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin sharhin da mabiya shafin suka yi a kasa:

Kara karanta wannan

Ka Daina Magana Ta Bakin Mataimaka, Yan Najeriya Na Bukatar Jin Muryarka, Sanatan APC Ga Buhari

yersmeen_m ta ce:

"Allah yasa saboda abun alkairin nan su sama zaman lfy Mai daurewa"

yam.jobe ta rubuta:

“MashaAllah abun ya taba zuciya sosai. Da fatan Allah SWT ya albarkace su kuma ya ba su ladan wannan aikin a cikin sabuwar rayuwarsu da tafiyarsu. Soyayya Daga Gambiya ”

khalil_foodies_and_chops ya yi sharhi:

"Shikenan an rufe bakin Yan sa' ido"

juwairiya_rufai ta ce:

"Masha Allah Allah saka masu da alkhairi"

Hotunan shagalin 'Luncheon' na auren Yusuf Buhari da amaryarsa Zahra Bayero

A baya mun kawo cewa a ci gaba da shagalin bikin dan shugaba Buhari Muhammadu na Najeriya; Yusuf da kuma 'yar sarkin Bichi Alhaji Nasiru Bayero; Zahra, an yi kasaitacciyar liyafar Luncheon a babban birnin tarayya Abuja.

A ranar juma'ar da ta gabata ne aka daura dauren masoyan biyu, inda aka samu haartar masoya daga sassa daban-daban na Najeriya da ma duniya baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel